Al’ummar unguwar Bachirawa karshen kwalta, sun koka kan harin da wasu Ƴan Daudu suka kai kan ofishin hukumar Hisbah na yankin Bachirawan da ke jihar Kano.
Dala FM Kano ta rawaito cewa, tun da fari ƙungiyar kare unguwar ne suka yi zargin wasu matasa da shiga kungiyar asiri, sakamakon ganinsu da misalin karfe uku na dare suna Ɗawafi a gidan tururuwa suna rokonta bakatunsu, inda suka watsa Nono da Gero da kuma Turare da sauran wasu kayayyaki akan gidan tururuwar, kamar suna Tsafi a wajen, lamarin da ya faru a ranar Juma’a.
- Sheikh Daurawa Ya Sauka Daga Muƙaminsa Na Shugaban Hisbah Kano
- G- Fresh Al’ameen Ya Roƙi Sheikh Daurawa Ya Janye Murabus Ya Dawo Kan Kujerarsa Ta Hisbah
Shugaban ƙungiyar kare unguwar ta Bachirawa Titin Jajira ƙarshen Kwalta, Abubakar Alhassan Datti, ya ce bayan an kori matasan an gano gidan da suka shiga wato gidansu wani Ɗan Daudu ne, inda suka mikawa Hisbah kayan daga baya kuma ƴan Daudun suka ragargaza motar hisbar wadda ta kawo dauki daga babban ofishinsu.
Daga karshe an yi zargin ƴan Daudun sunyi dandazo ɗauke da miyagun makamai, inda suka kai hari ofishin hisbar na unguwar Bachirawa akan lallai sai an saki mutanensu biyu da aka kama, da kuma bukatar a dawo musu da kayayyakin da mutanen unguwar suke zargin na tsafi ne.
Wannan dai na zuwa ne a ranar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sauka daga muƙamin shugabancin hukumar Hisbah ta jihar Kano, bayan kalaman gwamnan Kano akan yadda ya ce jami’an hukumar Maza suna kama ƴan mata suna watsawa a cikin mota lokacin da yake nuna takaicinsa a ranar Alhamis.
Wakilin Dala FM ya yi duk wani yunƙuri dan jin martanin ƴan Daudun amma abin ya ci tura.