Wasu ‘yan fashi sun kashe David Shikfu Parradang, tsohon Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) a Abuja.
Wani mai sharhi kan ayyukan masu tada kayar baya, Zagazola Makama, ya ce; majiyoyi sun bayyana cewa an sace Parradang ne da sanyin safiyar ranar Talata a kusa da yankin Area 1 na babban birnin tarayya.
- Bayan Cece-ku-ce Da Zelenskyy, Trump Ya Dakatar Da Tallafin Soji Ga Ukraine
- Kakaki: A Ko Da Yaushe Kasar Sin Tana Tsayawa Tare Da Kasashe Masu Tasowa
Rahotanni sun nuna cewa, an bi diddigin Parradang ne yayin da ya fito daga wani banki inda ya ciro kudi. Maharan sun kwace kudaden kafin daga bisani su kashe shi.
Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje.
Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS).
Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp