An kai wa mai tsaron ragar kasar Italiya da Paris St-Germain, Gianluigi Donnarumma da abokiyar zamansa hari tare da yi masa fashi a gidansu da ke birnin Paris kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Wasu gungun mutane ne suka kai harin inda suka daure su a gidansu da ke gunduma ta takwas a tsakiyar babban birnin kasar, kamar yadda majiyar ‘yansanda ta shaida wa kafar yada labaran Faransa.
Daga nan ne dan wasan da abokiyar zamansa suka tsere zuwa wani otal da ke kusa bayan maharan sun tafi kuma ma’aikatan otal ne suka sanar wa ‘yansanda kafin aka kai su asibiti.
Kakakin ofishin mai shigar da kara na birnin Paris ya shaida wa manema labarai cewa, an fara bincike kan zargin yin fashi da makami da wata kungiya da ta shirya ta kuma gudanar cikin dare a gidan Mista Donnarumma.
Rahotannin da ba a tabbatar da su ba a shafin yada labarai na Actu17 sun ce maharan sun yi awon gaba da kayan ado da agogo da kuma kayan alatu da kudinsu ya kai Yuro 500,000 (£430,000).
Dan wasan ya samu rauni kadan yayin da abokiyar zamansa, Alessia Elefante, ba ta samu rauni ba, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Farans.
Ofishin mai shigar da kara ya ce rundunar ‘yan sandan kasar Faransa ta musamman ta BRB da ke da alhakin yaki da fashi da makami, ya fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka shiga gidan dan wasan.
Gianluigi Donnarumma, mai shekaru 24, ya koma Paris ne shekaru biyu da suka wuce, kuma a ranar Juma’a ne ake sa ran zai hade da tawagar Paris St-Germain gabanin wasan sada zumunta na farko da kungiyar za ta buga da Le Habre da kuma rangadin kasashen Japan da Koriya ta Kudu.
Amma Donnarumma ba shi ne dan wasan kwallon kafa na PSG na farko da ‘yan daba ke kai wa hari ba, amma galibin hare-haren da aka kai a baya an yi su ne yayin da wanda aka kai ma harin ba su gida.
A watan Janairun da ya gabata, an yanke wa wasu maza biyu hukuncin dauri a gidan yari sakamakon wani hari da su ka kai a watan Maris din shekara ta 2021 a gidan dan wasan kwallon kafar Brazil Markuinhos da ke Ybelines a yammacin birnin Paris.
Markuinhos yana wasa a lokacin da lamarin ya faru amma mahaifinsa yana gidan tare da ‘ya’yansa mata guda biyu sai dai barayin sun bugi mahaifin a fuska da kuma hakarkarinsa amma bai ji rauni ba.
Kuma har ila yau a wannan ranar ce aka yi wa gidan abokin wasan Markuinhos Angel Di Maria fashi wanda shima ba ya gida kuma aka tafi da kayayyaki daban-daban kamar yadda rahotanni suka bayyana.