Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan wani kansilan karamar hukumar Funtua da ke jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari a unguwar Nasarawa da ke a karamar hukumar ta Funtua.
- ‘Yan Kasuwa 40 Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Kebbi
- Hutun Cikar Sin Shekaru 74 Ya Nuna Ci Gaban Da Kasar Ta Samu Da Wadatar Al’ummarta
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce bayanan da suka tattara sun tabbatar da mutuwar kansilan mai suna Samaila Buhari Mairago.
Iyalan mamacin sun ce tuni aka yi jana’izarsa a ranar Talata.
Funtua na daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaron ‘yan fashin daji a jihar ta Katsina.
Kuma yankin na makwabtaka da jihar Zamfara, wadda matsalar tsaron ke ci gaba da ta’azzara.