A jiya ne wasu mahara da ake zaton ‘yan fashin daji ne suka kai wani hari gonakin Sarki Gobir Adiya inda suka yi awon gaba da shanu sama da 200 da raguna da dama.
Babbar gonar wacce ta shafe sama da shekaru 40 tana da ma’aikata kusan 80 mallakin Alhaji Abdullahi S. Adiya, tana da ‘yan mitoci zuwa filin jirgin saman Sultan Abubakar III da tazarar kilomita 10 daga babban birnin jihar.
- Yadda ‘Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Mahajjatan Sakkwato Wuta
- ‘Yan Bindigar Da Suka Kai Wa Maniyyata Hari A Sakkwato Sun Kashe ‘Yan Sanda 6
Da yake bayyana wa wakilinmu harin, Alhaji Adiya ya ce dabbobin da aka sace su ne wadanda ake sa ran za a sayar da su domin bukukuwan Sallah mai zuwa.
A cewarsa, “Na bar gonar zuwa gidana, bayan tsakar dare kuma babu wani tunanin cewa za a kai wa gonar hari.
“A safiyar yau ne aka ta da ni, tare da labarin cewa an kai wa gonar hari, an kuma sace wasu garken shanu, raguna da tumaki da ake sa ran za mu sayar a wannan bikin na Sallah mai zuwa.
“Lokacin da aka garzaya zuwa gonar, bayanin da jami’an tsaro suka yi kawai shi ne, suna cikin shiri har karfe 3 na safe, sai kawai suka gano cewa an sace shanun da safiyar yau.
“Sun dawo da raguna goma sha takwas, da shanu goma sha bakwai, da bijimai biyu suna yawo a cikin daji. Asarar ba ta da iyaka. Muna magana ne game da satar dabbobi a cikin kewayon sama da ɗari biyu.”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Abubakar Sanusi, ya ce babu wani rahoton da aka kai wa ‘yan sanda kan adadin dabbobin da aka sace.
ASP Sanusi ya ce, “Lokacin da muka samu labarin harin, nan take muka tura mutanenmu gona. Sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a sanar da ku yadda ya kamata.”