‘Yan fashin daji sama da 100 ne suka tsere daga maboyarsu da ke dazukan yankunan Iche, Taka-Lafiya Gidan Makeri da Janjala a karamar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.Â
Sun tsere ne, bayan sojoji sun kutsa cikin dazukan da ke a karamar hukumar Kagarko.
- Wasu Matasa Sun Kone Ofishin Jakadancin Sweden A Iraki Kan Kona Alkur’ani Mai Tsarki
- An Rufe Makarantu A Kenya Saboda Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa
An ruwaito cewa yankuna da dama ne ‘yan bindiga suka mamaye a Kagarko, inda suke yin garkuwa da mutane a ‘yan watanni da suka gabata.
Sai dai an samu saukin sace-sacen mutane, biyo bayan sojiji sun tarwatsa mafakar tasu a dajin, tare da kuma cafke wasu da ake zargin masu kai wa ‘yan bindiga bayanan sirri ne.
An ruwaito wani mai rike da sarautar gargajiya a Kagarko Suleiman Aliyu, ya bayyana cewa sojojin sun shiga garin Kagarko a jiya Laraba da misalin karfe 11 na safe.
Aliyu, ya ce “sun shigo garin ne a cikin motocin su kirar Hilux da wasu manyan motoci wasu kuma akan babura, inda suka wuce kai tsaye zuwa cikin kauyen Iche, Taka-Lafiya, Gidan Makeri da Janjala har zuwa cikin dajin domin farautar ‘yan bindiga a dajin.
A cewarsa, bayan da ‘yan bindigar suka samu bayanan sirri sai suka tsere daga maboyar tasu.
Wata majiya a fadar sarkin Kagarko wadda ba ta bukaci a sakaya sunanta ba ta tabbatar da shigar sojojin cikin dajin.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar bai fitar da wata sanarwar kan lamarin ba.