Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bayyana ‘yan jaridar Nijeriya a matsayin babbar kariya ga kasar daga mulkin kama-karya, yana mai tabbatar da cewa ‘yancin manema labarai yana nan gaba-gaba a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, ya kara da cewa, ‘yan jarida sun taka rawar gani wajen daidaita rahotanni a lokutan da ake cike da ruɗani da ƙalubale.
Da yake jawabi a ranar Talata a taron shekara-shekara na 2025 da Babban Taron Shekara-shekara na Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) a Najeriya a Abuja, Shettima ya tabbatar da jajircewar gwamnatin tarayya na bai wa masu aikin yada labarai kariya daga masu cin zarafi ko barazana.














