Wani rukunin mai kunshe da ‘yan jarida 22 daga kasashe 17, ya yaba matuka da ci gaban jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, yayin ziyarar kwanaki 9 da rukunin ya kai jihar.
Yayin ziyarar ‘yan jaridar daga ranar 21 zuwa 29 ga watan Satumba, sun ganewa idanunsu yanayin ci gaban tattalin arziki da zaman takewar jihar, da mabambantan al’adu da yadda aka raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Sun kuma ziyarci wurare da dama, ciki har da Urumqi, babban birnin jihar da yankin Kashgar da yankin Ili na Kazak mai cin gashin kansa.
- An Yabawa Ci Gaban Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin Yayin Liyafar Da Aka Shirya Domin Murnar Cikarta Shekaru 74 Da Kafuwa
- Jama’a A Fadin Kasar Sin Na Bikin Ranar Kafuwar Kasar Yayin Da Suka Shiga Lokacin Hutu Mai Tsawo
A babbar kasuwar kasa da kasa ta Urumqi, Simon Max Zeise, mai tace labaran harkokin kasuwanci na kafar yada labarai ta Berliner Zeitung, na ganin kasuwar a mastayin alama ta ci gaba. Ya ce yayin ziyarar, ya ga hakikanin jihar Xinjiang. A cewarsa, “ A Jamus, akwai mutanen dake rayuwa a kan titi. Amma a Xinjiang, ba ka ganin alamun talauci, kuma mutane ba sa rayuwa a kan titi. Suna da ayyuka, suna samun ilimi, kuma al’umma na cin gajiyarsu.”
Tun a zamanin da, Xinjiang yanki ne mai dauke da kabilu mabambanta. ‘Yan jaridar sun yawata titunan tsohon birnin Kashgar, tare da ganin al’adun gargajiya masu ban sha’awa. A cewar Mohammad Reza Noroozpour, mataimakin kamfanin dillancin labarai na Khabaronline na kasar Iran, “Xinjiang wuri ne mai cike da mabambantan al’adu da addinai da kabilu masu ban sha’awa. Muna farin cikin ganin yadda dukkan wadannan mabambantan al’adu ke rayuwa tare cikin lumana.”
‘Yan jaridar sun kuma ziyarci kwalejin horar da malaman addinin musulunci dake birnin Urumqi, da masallacin Id Kah a Kashgar. Shugaban kafar yada labarai ta Daily Scrum ta kasar Canada, Donovan Ralph Martin, ya ce “hakika akwai ‘yancin bin addini a Xinjiang. Duk wanda ya fadi akasin hakan, to jahili ne.” (Fa’iza Mustapha)