Ya zuwa ranar 1 ga watan Mayu, yawan ‘yan kasuwa daga kasashe da yankuna sama da 215 da suka halarci bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasa da kasa na kasar Sin, wato “Canton Fair” karo na 135, ya kai 221,018, wanda ya karu da kashi 24.6 cikin dari bisa makamancin baje kolin da ya gabata.
Girman harabar baje kolin Canton Fair na wannan karo ya kai murabba’in mita miliyan 1.55, yawan rumfuna ya kai kusan dubu 74, kamfanonin da suka halarta sun kai dubu 29.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp