Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kara bai wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, lokaci wajen magance matsalolin da ke addabar kasar.
Ya kara da cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta fara magance duk wani rikicin da aka gada a sassa daban-daban.
- Tinubu Ba Zai Yi Murabus Ba, inji Ministan Yaɗa Labarai
- Za Mu Ɗauki Mataki Kan Duk Masu Sukar Shugaba Tinubu Kan Tattalin Arziƙi – Bello Matawalle
Gowon ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Laraba a Abuja.
“To, ina fada masa cewa babu wani shugaban Nijeriya da zai kai matsayinsa kuma a ce ba zai samu dukkan rahotonni kan abin da ake fada a kansa ba.
“Amma hakika, babu shakka daga abin da mutum yake ji da abin da yake gani a kafafen yada labarai daban-daban. Ina ganin gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalolin da ke addabar kasar.
“Ina ganin duk abin da mutum zai iya cewa shi ne ‘yan Nijeriya dole ne mu bai wa shugaban kasa lokaci don a yi abubuwa da gaske. Kuma ya yi wuri a ce za a samu cikakken sakamako a yanzu.”
Gowon ya ce ganawar da shugaban kasar ta ta’allaka ne kan batun kalubalen da ke addabar yankunan ECOWAS, inda ya ce dole ne a sasanta.
“A matsayina na shugaba mai raye, ko kuma uban kungiyar ECOWAS, ina ganin sai mun tattauna wasu tsare-tsare domin ganin abin da za a iya yi don shawo kan lamarin,” Cewar Gowon.
Ya karyata ikirarin da aka yi a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa ya ki halartar taron da kungiyar ECOWAS ta shirya, inda ya kara da cewa watakila hakan ya faru ne saboda rashin sadarwa.
“Ina ganin idan akwai wata rashin jituwa sai shugaban kasa ya kira ni domin mu tattauna abin da zan yi.”