Kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 104.16 na da lambar shaidar zama dan kasa wato National Identification Numbers (NIN) zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2023, kamar yadda bayanan da hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC) ta fitar.
A cewar bayanin, jihar Legas ce kan gaba wajen yawan mutanen da suke da lambar shaidar a fadin kasar nan da suka kai mutum miliyan 11.42. Yayin da kuma jihar Kano ta mara mata baya da yawan mutum 9.19 masu shaidar NIN.
- Tinubu Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatar Jin Kai Kan Zargin Karkatar Da Miliyan N585
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Alex Otti A Matsayin Gwamnan Abia
Fitattu kuma manyan jihohi biyun a cewar bayanan da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) su ne na gaba-gaba wajen samun lambar NIN tun lokacin da aka fara aikin samar da shaidar ga ‘yan Nijeriya.
Sauran jihohin da suka kasance na gaba-gaba wajen shiga sawun masu mallakar shaidar sun kunshi Kaduna mai miliyan 6.45; Ogun miliyan 4.40; Oyo miliyan 4.04; Katsina miliyan 3.54; birnin tarayya (FCT) mai miliyan 3.51; jihar Ribas miliyan 3.13; Delta miliyan 2.79 da kuma jihar Bauchi mai mutum miliyan 2.76 da ke da lambar shaidar zama cikakken dan kasa.
Kazalika, bayanan na NIMC na nuni da cewa jihohi 10 da suke matakin kasa kasa a samun shaidar NIN sun hada da Kwara mai miliyan 1.77; Akwa-Ibom mai miliyan 1.76; Kogi mai miliyan 1.73; Enugu mai miliyan 1.67; Yobe mai miliyan 1.65; Taraba mai miliyan 1.49; Kurus Ribas miliyan 1.19; Ekiti miliyan 1.02; Ebonyi mutum 839,506 ke da lambar yayin da jihar Bayelsa mutum 657,484 ke da lambar shaidar.
A gefe guda, sabowar darakta janar na NIMC, Injiniya Abisoye Coker-Odusote, ta bayyana cewar, hukumar ta himmatu da kara hanzarta wajen yin amfani da zamani wajen samar da shaidar tantancewa ga mutane a cikin manufofin shugaban kasa Bola Tinubu na sabunta fata ga ‘yan kasa.
A cewar Coker-Odusote, “NIMC ta maida hankali wajen ayyukan da ke gabanta na saukaka samar da shaidar kasa da suka kunshi lambar shaidar zama dan kasa NIM, da inshura, katin shaidar inshura e-ID, shaidar tantancewa gami da tantance bayanai da tabbatar da su. Ya kamata a lura a wannan zamanin na fasaha, shaidar tantancewa na gaba-gaba wajen saukaka gudanar da shirye-shirye.”
“Sannan, lambar tantancewa na bai wa gwamnati damar gabatar da tsare-tsare da shirye-shiryen ingantawa da bukasa rayuwar al’umma hadi da tsarin hidimar kudaden da za su taimaka wajen gudanar da lamura. Kazalika, tantancewar na taimaka wa gwamnati wajen gudanar da mulkin gaskiya da adalci hadi da shigo da kowa cikin sha’anin gudanar da mulki.”
Dangane da wahalhalun da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke sha wajen mallakar shaidar NIN kuwa, darakta-janar din ta bada tabbacin cewa za a shawo kan dukkanin matsalolin da suke akwai kuma za a yi kaddamar da bincike domin gano matsalolin da suke akwai da shawo kansu domin ‘yan Nijeriya su ke samun lambar a kan lokaci.