Bankin Stanbic IBTC ya yi nasarar sanya farin-ciki ga masu ajiyr kuɗi su kimanin 148, inda bankin ya raba masu Naira milyan 23 daga tsakanin watan Mayu da Yuni bayan da aka zaɓi waɗanda suka yi nasara wajen ajiya har sau 4 a karo na 4 garaɓasar gasar da bankin ya sanya a garabasa ta biyu da ta uku duk a cikin watan, tare kuma da ƙaddamar da garabasar da ake yi duk bayan wata huɗu a shekarar 2025, lamarin ya yi matukar sauya rayuwar mutane a sassa daban-daban na Nijeriya.
Irin wannan taimakon da ake yana ci gaba da bunƙasa duk ajiyar da aka yi a kowace rana zuwa wani babban mataki wadda hakan zai ƙara janyo hankalin mutane su yi koyi da hakan da kuma sabawa da ajiyar kuɗi a banki.
- PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi
- ’Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 6 A Taraba
A zaɓen fitar da zakarun da suka yi nasara daga watannin Mayu da Yuni da aka yi a hedikwatar Bankin Stanbic IBTC da ke Legas inda masu ajiya su kimanin140 kowane daga cikinsu ya samu Naira 100,000, wato Naira milyan 14 na kyautukan kuɗi.
A ƙarƙashin jagorancin hukumomin da suke lura da yadda aka tafiyar da abin, da suka hada da hukumar kula da yadda ake tafiyar da gasa da kuma kare masu amfani da kaya (FCCPC) da kuma cibiyar kula da yadda ake tafiyar da harkokin tallace – tallace ta Nijeriya (ARCON), sai kuma hukumar kula da harkokin kallo- kallo, da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA), zaɓen fitar da waɗanda suka cancanta an yi shi cikin gaskiya da adalci, inda ake saka wa waɗanda suka ajiyar kuɗi, kuma suka yi hakurin barin har naira 10,000 a cikin asusun ajiyarsu na Bankin Stanbic IBTC ko kuma a @ease Wallet har zuwa kwana 30.

Daga mata ‘yan kasuwa zuwa ‘yan makaranta ɗalibai da kuma waɗanda suka yi ritaya daga aiki da waɗanda suka samu nasara a yanzu sun zarta na baya domin suna iya biyan kuɗin makaranta, su kuma yi karamar sana’a, ko iya tafiyar da buƙatunsu na gida.
Sun samu ƙarin farin ciki da aka samu wasu mutane takwas daga waɗanda aka fitar da suka cancanta na watanni huɗu na farkon shekara, wanda aka yi a rana ta bakwai.
Mutane bakwai ne suka samu nasara, sai kuma mutum daya daga kowace shiyya ya samu Naira milyan ɗaya; yayin da kuma ita babbar kyauta da ake yi duk bayan wata hudu, mutumin da yayi nasara ya ke tafiya gida da Naira milyan biyu, gaba ɗaya kuɗinsu sun kai Naira milyan tara.
Duka hanyoyin da aka bi domin samun waɗanda suka yi nasara ya nuna irin yadda Bankin Stanbic IBTC, ya ɗauki kowane mai ajiya da Bankin da muhimmanci.
Zaɓar waɗanda suka cancanta da ba a daɗe da yinsa ba na bayar da lada ko kyauta saboda ajiyar kuɗi da aka yi a watan Mayu 2025, wanda tuni aka kashe Naira milyani 30 wadda aks raba a tsakanin mutanen da suka yi nasara su 218 a karo na huɗu, sai kuma fiye da Naira milyan 300 da aka ba mutane fiye da 2,000 da suke da asusun ajiya a bankin, an fara tsarin bayar da kyauta ga masu asusun ajiya tun a shekarar 2021. Bankin Stanbic IBTC yana taimakawa rayuwar ‘yan Nijeriya.
Emmanuel Aihevba, shi ne Shugaban Bankin Stanbic IBTC a Nijeriya, ya ce wani abu dangane da kyautar da aka bayar da kuma yadda aka zaɓi waɗanda suka yi nasara a wannan shekarar.
“Bikin zaɓar waɗanda suka cancanta a ba su kyautar da yadda aka aiwatar da shi a wata biyu, har ma wanda aka yi na farkon wata huɗu na wannan shekarar na bayar da kyauta saboda ajiyar kuɗi a karo na huɗu an yi bikin nuna farin ciki ne ga waɗanda suke hulɗar ajiya a banki da mu kan yadda suka mayar da hankalinsu kan lamarin. Mun saka wa masu hulɗa da mu su 148 da zunzurutun kuɗi har Naira milyan 23 saboda yadda suka amince da tafiya da mu, su yi amfani da su kan lamarin da ya shafi ilimi ko wata sana’a.

A Bankin Stanbic IBTC, muna nuna cewa abokan hurɗarmu na banki ya dace muma mu saka masu wajen samar masu da wasu damarmakin da za su taimaka masu su bunƙasa rayuwarsu da kuma koya masu sabo da al’adar ajiyar kuɗi a faɗin tarayyar Nijeriya.”
Kesena Igben, mutumin da ya yi ritaya ya kuma yi nasarar lashe kyautar wata, ya nuna jin daɗinsa inda yace: “Na zo tare da ‘yata domin na amshi kyauta ta. Muna kan hanyarmu ta zuwa ofishin Stanbic IBTC, sai ta ce, ‘Baba, na ga kana farin ciki. ’Sai na ce ma ta, ‘Ko kin san cewa wannan kuɗin zai taimaka mani wajen sayen man fetur na mako biyu ?’ Don haka a gare ni, samun kuɗin nan da Bankin Stanbic IBTC suka bani, ya raba ni da tunanin yadda zan samu kuɗin da zan sayi fetur na mako biyu, wannan wata babbar alfarma ce gare ni.”
Yadda Stanbic IBTC ya nuna damuwarsa kan farin cikin abokan hulɗarsa, abinda ya ke nuna adalcin haka a fili shi ne’ yadda aka sakawa masu ajiyar kuɗi “abubuwan da aka yi cikin gaskiya da adalci, hukumar kare masu amfani da kaya ”ta samu kyautar ARCON a shekarun 2023 da kuma 2024.
Don haka kai ma shiga cikin annashuwa! Ajiye Naira 10,000 kacal ko fiye da haka har zuwa kwana 30 ko fiye da haka a asusun ajiya na Stanbic IBTC ko kuma @ease Wallet domin ka samu damar shiga bikin zaɓar waɗanda za su samu na gaba.
Shiga kafar sadarwa ta https://smebanking.stanbicibtc.com/AccountOpening/tier-one ko kuma ka ziyarci wani Bankin ka fara daga yau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp