Abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan sun nuna ƙarara ‘yan siyasarmu ba komai suke yi ba illa wasan kwaikwayo da rayukan mu ‘Yan Nijeriya, don haka kowa ya san alƙiblar da zai bi. Shugaban Gamayyar Matasan Arewa a Kudancin Nijeriya da ke Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya furta haka domin nuna damuwarsa kan zubar da jini da nakasta ‘yan arewa da ake ci gaba da yi a kullu yaumin.
- 2023: Duk Sanatocin Bauchi Masu Ci Babu Mai Komawa Sun Sha Kaye A Mazabunsu
- 2023: Jm’iyyar APC Ta Fara Tantance Masu Neman Takarar Shugabancin Nijeriya
Ya bayyana haka ne yayin da yake kokawa a wata sanarwa ga manema labarai inda ya yi bayanin cewa, “yadda shugabannin siyasar ƙasarmu Nijeriya suke cutar da al’ummar ƙasar nan wanda duk mai hankali da hangen nesa ya kamata ya ba wa kansa amsa, abin dubawa ne. Domin yadda ‘yan siyasa suke wasan kwaikwayo da ‘Yan Nijeriya ya zama wajibi ne kowa ya san inda ya dosa, sun bari ana ta asarar rayuka ba-ji-ba-gani amma siyasarsu kawai suka sa gaba. Ɗan arewa ya zama Ɗanbora, an ware shi a ƙasar nan bai da wani kataɓus. A kashe shi, a tafi da iyalinsa, a sace dukiyarsa duk babu mai nuna damuwa a cikin waɗannan ‘yan siyasar illa sha’anin gabansu kawai. Waɗanne irin mutane ne muke da su a matsayin shugabanni? Jinin ɗan arewa yana kwarara amma kowa siyasarsa kawai ya sa gaba.
“Duk wani babba da ya ce yana tare da talaka ya zama abin ƙyama a gun ɓata-garin shugabannin Nijeriya, ina jami’an tsaronmu masu kishin Nijeriya? Kuna ina ne ake yi wa ƙannenku da iyayenku kisan gilla babu wani shugaban da ke yin magana? Dan haka muna kira ga matasa da sauran ƙungiyoyin ‘yan arewa da mu nema wa kanmu mafita tun kafin lokaci ya ƙure mana.” In ji shi.
Alhaji Ibrahim ya kuma nuna damuwa a kan rashin ‘yanto mutanen da aka sace ana garkuwa da su waɗanda ya ce Allah kaɗai ya san irin azabar da suke sha a hannun ‘yan ta’adda.
Ya ƙara da cewa, “ina mutanen da aka sace a jirgin ƙasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, tambaya a nan ita ce idan kwangila waɗansu suka karɓa don a yi mana wannan kisan mummuƙe a fito fili a yi mana bayani, domin yadda ɗan arewa ya zama a ƙasar nan a yau dabba ta fishi daraja, cin zarafin ya yi yawa mutaƙar gaske. Don haka muna mkira ga ‘Yan Nijeriya musamman ‘yan arewa mu san su waye za mu mara wa baya da za su zama mana tudun tsira a zaɓen 2023, idan ba haka ba, za mu ci gaba da zama jiya-i-yau kuma ba za mu yarda da hakan ba.” Ya bayyana.