Tsohon Shugaban Nijeriya na Mulkin Soji, Janar Abdulsalami Abubakar, ya nuna damuwa game da tsananin wahalar tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan.Â
Ya yi gargadin cewa yanayin na kara tsananta wanda ya jefa ‘yan Nijeriya da dama cikin matsin rayuwa.
- Yahaya Bello Ya Amsa Gayyatar EFCC
- Majalisar Dinkin Duniya Ta Bai Wa Maiduguri Tallafin Dala Miliyan 6
Da yake magana a gidansa da ke Minna, a Jihar Neja, Janar Abubakar, ya bayyana cewa mutane na gaza xin abinci sau uku a rana, kuma hauhawar farashin man fetur, kudin makaranta, da sufuri na kara tabarbarewa.
Ya ce bai kamata a dogara da tallafi kadai ba wajen magance matsalar, inda ya bukaci gwamnati ta dauki matakai masu tsauri.
Abubakar ya bayar da shawarar cewar akwai bukatar gwamnati ta sanya hannu wajen saukaka farashin abinci.
Ya yi kira ga gwamnati da ta sayi kayan abinci sannan ta sayar da su ga jama’a a farashi mai rahusa don saukakawa talakawa.
Bugu da kari, Abubakar ya yi kira ga matasan da ke shirin zanga-zangar #EndBadGovernance ta ranar 1 ga watan Oktoba da su yi cikin lumana.
Ya ja hankalin jama’a game da illar tayar da tarzoma da sace-sacen da suka faru a lokacin zanga-zangar da ta gabata.
Ya jaddada muhimmancin kaucewa aikata laifuka yayin zanga-zanga.