Sakamakon yawaitar ayyukan garkuwa da mutane a cikin Babban Birnin Tarayya Abuja a ‘yan kwanakin nan da ma wasu sassan Nijeriya, lamarin da ya ta da hankalin al’umman kasa da firgitasu.
‘Yan Nijeriyan na kara shiga damuwa a yayin da suke yekuwar a tabbatar da an zakulo ‘yan ta’addan da kuma masu daukan nauyinsu a matsayi wani mataki na kawo karshen matsalolin garkuwa da mutane da neman kudin fansa.
- Jami’an Tsaro Sun Yi Dirar Mikiya Gidan Dakta Idris Dutsen Tanshi
- Gwamnatin Zamfara Zata Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata
Tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya shaida a shafinsa na D cewa, za a iya ganowa da samu wadanda suke amfana da makuden kudaden da jama’an kasa ke biya da sunan fansa a duk lokacin da aka sace musu wani nasu.
Ya nuna gayar takaicinsa kan ayyukan ‘yan ta’addan masu garkuwan da mutane da karban miliyoyin daruruwa a hannun jama’a, yayin da kuma suke kunsa musu damuwa da takaici hadi da bakin ciki a duk lokacin da suka sace wani ko wasu.
“Su masu garkuwan mafiya yawansu yara ne wasu ma ‘yan kasa da shekara ashirin. Babu wani alamar morewa ko jin dadi a tattare da su, hatta kayan da suke sanyawa ba za ka ga wani alamin kayan more rayuwa a tattare da su ba, duk kuwa da makuden kudaden da suke amsa a hannun jama’a.
“Tambayar a nan shi ne, su waye ke amfana da makuden kudaden da wadannan masu garkuwa da mutanen ke amsa? Kuma su waye ke samar musu da makamai da suke samun damar gudanar da ayyukan ta’addanci da su?,” Sanatan ya tambaya.
Rahotonni sun zo a baya-bayan da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Sani Muhammad Takori ya yi zargin cewa, ayyukan ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara na samun goyon baya daga wasu jiga-jigan mutane.
Kazalika, a baya-bayan nan in za a iya tunawa, gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang, ya fito balo-balo ya ce, jami’an tsaro sun san wadanda suke amfana da aikace-aikacen ta’addanci a jihar.
Da yake ganawa da wata gidan talabijin, gwamnan wanda ke maida bayani kan hare-haren baya-bayan nan a jihar da ya lakume rayukan mutum sama da 200, ya ce, su ma ‘yan ta’addan an san su.
“Abun da zan iya fada muku kan kashe-kashe da hare-haren Filato a baya-bayan nan tsagwaran ta’addanci ne.
“Na yi imanin masu daukan nauyin ‘yan ta’addan nan da masu cin gajiyar ta’addancin da masu dauke da makaman an sansu. Jami’an tsaro sun sansu, sun san maboyarsu. Wannan dalilin ne ya sa muka nace kan cewa dole ne hukumomin tsaro su yi aikinsu, su tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma,” ya shaida.
Wani masanin harkokin tsaro, Mista Akogwu John, ya nuna matukar mamakinsa kan yadda hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya suka yi gum kan wannan ikirarin na gwamnan Filato.
Ya ce, “Gwamnan Filato ya fito baro-baro ya ce hukumomin tsaro sun san wadannan mutanen wadanda suke haifar da wannan matsalar a ko’ina. Ban ga labarin yadda hukumomin tsaro suka karyata wannan ikirarin ba. Kenan akwai kamshin gaskiya.
“Muna rayuwa a kasar da komai ana wasu da shi har da lamarin tsaro. Su waye wadannan jiga-jigai mutane masu karfin da ke daukan nauyin kashe-kashen mutanen da ba su ji ba su gani ba kuma me ya sa gwamnati ta yi gum da bakinta?” ya tambaya.