ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Allah Ya Amintar Da Zuciyar Manzon Allah (SAW) Tare Da Tausasawa

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 years ago
Manzon Allah

Assalamu alaikum, masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata muna bayani ne game da yadda Allah yake tausasawa idan zai yi magana da Manzon Allah (SAW), musamman ayar da Allah ya ce masa (SAW), “Allah ya yafe maka, me ya sa ka yi musu izini (cewa su zauna)”.

Idan ba a manta ba, za a tafi Yakin Tabuka ne sai munafukai suka zo wurin Annabi (SAW) ya yi musu afuwa kar su tafi yakin, sai Annabi (SAW) ya karbi uzurinsu saboda Allah ya ba shi zabi a kan hakan. Allah Ta’ala ya ce, “idan suka nemi izininka cikin wani sashe na sha’aninsu; ka yi wa wanda ka ga dama a cikinsu”.

  • Manzon Musamman Na Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Liberia
  • Manzon Musamman Na Shugaban Sin Zai Halarci Taron Koli Karo Na 19 Na Kungiyar Kasashe ‘Yan Ba-Ruwanmu

To sai ya yi musu uzuri su zauna a gida kar su tafi yakin, shi ne sai Allah yake ce masa Allah ya yafe maka amma me ya sa ka yi musu uzuri kar su tafi yakin. A karshen ayar Allah ya ce “ai da ka jira har sai masu gaskiya (muminai) sun bayyana gare ka kuma ka san su wanene ke karya.

ADVERTISEMENT

Malam Alkadiy Iyad ya ce idan aka dubi wannan ayar, ya wajaba ga Musulmin da yake tarbiyyantar da zuciyarsa da ragamar Shari’a (tun ma ba wanda ya ce shi malami ne ba) ya rika ladabtuwa da ladabin Alkur’ani. Ma’ana kar ya dinga yin hukunci da fadar abin da ya ga dama, ya dinga lura da yadda Alkur’ani yake fadar magana musamman ma idan maganar ta shafi Annabi (SAW) da sauran Sahhabansa masu girma har zuwa kan malaman al’umma. Idan magana ta zo, kar mutum ya dinka kwakule-kwakule a ciki wai don shi yana so sai ya tona komai. Da yawa wasu daga cikin mutane idan ba su ji abu daga bakin malami ba babu ruwansu da shi amma idan suka ji a wurinsa shikenan, walau sun gane ko basu gane ba kawai za su yi amfani da fahimtarsu wurin yiwa abin hukunci bisa kafa hujjar cewa malami ne ya fadi abin. Idan laifi ne ko kuskure ka ga an dora al’umma kan wata turba da ba ta dace ba.

Alkur’ani yana da alkunya, misali; a kan maganar saduwa da mace sai ya sakaya abin ya ce “shafar mace”, malamai idan suka zo fassara sai su yi bayani cikin hikima a kan saduwa. Idan wurin lalata da maza ne ma Alkur’ani sai ya sakaya ya ce “wadanda ke zuwa wa maza maimakon mata”, bai fito da abin karara ba saboda koyar da mu dattaku. Bai kamata a yi ta warware magana babu ladabin Shari’a da koyi da ladabin Alkur’ani ba. Idan kana karatu sai ka zo wurin da aka taba manya, to ko ka ga laifin da aka ce an yi; ka yi kokarin yi masa mafita; idan ba za ka iya ba ka kame bakinka in ko ba haka ba a maimakon gyara sai mutum ya yi barna. Fir’auna kafirin da ya ce shi Allah ne, Allah ya umurci a fada masa magana mai dadi a cikin Alkur’ani. Allah ya ce wa Annabi Musa (AS) da Annabi Haruna (AS) su fada wa Fir’auna magana mai dadi ko zai wa’azantu. To ina ga wanda laifinsa ko rabin na Fir’auna bai kai ba fa? Rashin bin ladabin Alkur’ani duk ya ja mana shiga cikin halin da muka fada yau. Mutum don ya ce shi Musulmi ne ko malami ko almajiri, sai ya rika fadin abin da ya ga dama a matsayin addini ko ya yi hukunci yadda ya ga dama ga kowa, abin har ya wuce maganar baki ya kai ga daukar makami ana kashe jama’a. Duk rashin bin ladabin Alkur’ani ya kawo mana haka. Ba mu gyara bakinmu ba kuma idan baki bai gyaru ba zuciya ba za ta gyaru ba. Mu yi kokarin bin ladabin Alkur’ani cikin maganganunmu, da gogayyarmu, da ba da amsoshin tambayoyi a cikin karatuttukanmu.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

Alkur’ani shi ne kololuwar sannai (jam’in sani), shi ne dausayin ladabai na addini da na duniya baki daya. Musulmi ya dinga kula da wannan tausasawa mai ban mamaki cikin tambayar da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a wannan ayar ta “Allah ya yafe ma, me ya sa ka yi musu izini, (Ma’ana Allah zai tambayi Manzon Allah (SAW) ne amma sai da ya hada tambayar da afuwa). Lallai mutum ya rika lura da fa’idodin ladabi da ke cikin ayar. A lura cewa, Allah (SWT) sai da ya fara da afuwa kafin tambayar ta rarauka. Kuma koda ma wadanda suke ganin Annabi (SAW) laifi ya yi Allah yake masa ‘fada’ a cikin ayar, to ai Allah ya ce ya yafe kuma yafiyar aka fara ambata kafin rarauka din. Wannan yana kara tabbatar da cewa babu wani laifi a cikin izinin da ya bayar (SAW). Allah ya kara amintar da zuciyar Annabi (SAW) daga tsoron a ce masa ya yi laifi kafin a tambaye shi cewa “me ya sa ya yi musu izini?”.

A cikin wata ayar Allah (SWT) yana cewa “ba domin mun tabbatar da kai ba (ya Rasulallah) ka kusa karkata kadan zuwa gare su”. Wani sashe na malaman Tafsiri sun ce Allah ya yi wa Annabawa (Alaihimus salam) rarauka da yawa, amma sai bayan da suka yi tuntube da abin da suka yi sannan Allah ya yi musu raraukar. Amma shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) ta bangarensa, rigakafin ya ji a ransa cewa ya yi laifi Allah ya yi masa. Manzon Allah shi ne mafi kiyaye dokokin Allah da soyayyarsa saboda Allah ya ce “ba domin mun tabbatar da kai ba ka kusa ka karkata kadan zuwa gare su”. Wannan yana nuna Allah ne da kansa ya jibinci lamarin tabbatar da kiyaye Manzon Allah (SAW) daga barin aikata abin da za a yi masa rarauka a kai. A cikin rashin tsoratar da shi sai Allah ya kubutar da shi. Misalin yadda za a fahimci haka shi ne, wani dan kasuwa ne ya koya wa wani mutum kasuwanci, bayan dan wani lokaci sun zo suna hira sai wannan dan kasuwan ya ce wa mutumin “ba domin na koyar da kai kasuwancin nan ba; da ka zubar da jarin da na baka”. Ma’anar wannan maganar tana nufin salwantar da jarin nan abin tsoro ne kuma hakan ba ta auku ba bisa dalilin koyar da wannan mutumin kasuwancin da yake yi.

To Allah ya kiyaye Manzon Allah (SAW) ga barin karkata zuwa ga mutanen nan kasancewar shi da kansa (SWT) ya tabbatar da shi ta yadda ba zai yi hakan ba. A cikin ba shi tsoro (na barin tarku aula) sai Allah ya girmama shi tare da darajanta shi.

Yana daga irin wannan magana fadin Allah cewa “Hakika mun sani abin da kafiran nan suke fada maka yana bata maka rai, sai dai ba su danganta ka da karya (ko ba sa karyata ka, a wata kira’ar) sai dai azzaluman nan (kafirai) suna jayayya ne da ayayoyin Allah”. Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) ya ce sanadin saukar wannan ayar shi ne: Abu Jahli ne ya ce wa Annabi (SAW) “Muhammadu; mu fa ba ma karyata ka, mun san kai maigaskiya ne, abin da ka zo da shi ne ba mu yarda da shi ba muke karyatawa.” An ruwaito cewa a yayin da mutanen Annabi (SAW) suka karyata shi sai Annabi ya yi bakin ciki, sai Jibrilu (AS) ya zo masa ya ce “me yake bata maka rai (ya Rasulallah)?”, sai Annabi (SAW) ya ce “mutanena ne suka karyata ni”, sai Jibrilu ya ce masa “mutanenka sun san kai mai gaskiya ne, ba da kai suke ba; da ayar Allah suke”, daga nan sai Allah ya saukar da wannan ayar.

A cikin ayar akwai macira mai saukin riko cikin bai wa Manzon Allah hakuri da shafar zuciyarsa cikin lallashi cewa Allah ya tabbatar Manzon Allah mai gaskiya ne, haka nan ma a wurin kafiran domin da kansu sun furta cewa shi (SAW) mai gaskiya ne tare da kudurce hakan har ya zamo suna kiran sa da sunan Aminu (Amintacce) tun kafin Annabta. Allah ya dauke wa Manzon Allah (SAW) damuwar zuciyarsa ta hanyar tabbatar da cewa hatta su kansu kafiran sun san shi (SAW) mai gaskiya ne. Kuma sai Allah ya sanya zargin (karyar) ga kafiran ta hanyar ambatar su da sunan masu jayayya da ayoyinsa kuma azzalumai.

Manzon Allah
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Next Post
GORON JUMA’A

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

July 7, 2026
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

ADC Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 17 Cikin Yunwa

July 7, 2026
Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

July 6, 2026
Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

July 6, 2026
Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

July 6, 2026
Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

July 6, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Montenegro Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 7, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 6, 2026
Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

July 6, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.