Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce ‘yan Nijeriya ba su da sha’awar manyan jam’iyyun siyasar kasar nan guda biyu – PDP da APC, kawai suna neman canji ne.
Obaseki yayin da yake hira da gidan Talabijin na AIT, bayan Kammala zaben gwamnan jihar Ekiti, ya bayyana cewa makomar siyasar kasar nan tana canzawa.
A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta na Instagram na hamshakin attajirin nan, Dele Momodu, gwamnan Edo ya ce, “Ta yaya PDP a tarihin ta na girma ace ba tayi nasara Ba? Ba ta zo na biyu ba ma.
Don haka, za ku iya ganin cewa wani abu yana faruwa. Makomar siyasarmu a kasar nan tana canzawa.
Shima da yake tsokaci kan zaben Ekiti, wani jigo a jam’iyyar, Tom Ikimi, ya bayyana cewa jam’iyyar ta sha kaye ne saboda muggan ayyukan tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp