Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya NERC, Sanusi Garba, ya ce ‘yan Nijeriya za su shaida yadda aka inganta wutar lantarki daga ranar 1 ga watan Yuli bayan kokarin da masu ruwa da tsaki a masana’antu suka sake yi.
Garba ya ba da wannan tabbacin ne a wata tattaunawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki a bangaren wutar, a ranar Laraba a Legas.
Taron ya samu halartar manyan jami’an NERC da TCN da Kamfanoni masu samar da wutar lantarki da kuma Kamfanonin Rarraba Wutar.
Ya ce NERC ta samar da wata yarjejeniya ta kwangila tsakanin Gencos da TCN da kamfanonin DisCos 11 da za su ba da tabbacin samar da wutar lantarki, watsawa da kuma rarraba wutar mai nauyin akalla megawatt 5,000 a kullum ga ‘yan Nijeriya daga ranar 1 ga watan Yuli.
A cewarsa, sabuwar yarjejeniyar ta ta’allaka ne akan dukkan kamfanonin masu ruwa da tsaki Kan harkar wutar lantarki, za kuma a hukunta duk wanda ya Saba wannan sabon tsarin da aka gindaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp