‘Yan Nijeriya sun sha alwashn maka gwamnatin tarayya a kotu bisa amincewa da ta yi da karin kudin kiran waya da data da sauran caji-cajin da kamfanonin sadarwa ke yi.
Kwatsam sakamakon wannan lamarin, masu hada-hadar kudade ta PoS sun kara kudin cazan jama’a da suke yi.
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
- Jagoranci Nagari: Kungiyar Lauyoyi Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo
Shugaban kungiyar masu amfani da layukan sadarwa, Adeolu Ogunbanjo da kuma jami’in watsa labarai na kungiyar masu mu’amala da kudade ta wayar tarho da wakilansu na bankuna a Nijeriya, Ogungbayi Ganiyu su ne suka tabbatar da shirin garzawa kotu a hirarsu da ‘yan jarida a ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne dai bayan sahalewar da hukumar kula da sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayar ga kamfanonin sadarwa da su kara kudaden cajin da suke yi da kaso 50 a cikin 100.
Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Bosun Tijani, shi ne ya amince wa kamfanonin da su yi karin biyo bayan zaman da suka yi da shi da suka nemi yin karin kaso 100 na cajin da suke yi ga al’ummar Nijeriya.
Wannnan karin kuma na zuwa ne bayan shekaru 13 tun bayan da NCC ta sanar da farashin jaddawalin cajin da kamfanonin za su yi a shekarar 2013.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa da wannan sabon karin na nuni da cewa kamfanonin za su cazan ‘yan Nijeriya naira 16.5 a kowace kiran waya na minti daya daga naira 11, yayin da tura sakon kar-ta-kwana ya koma naira 6 daga naira 4, sannan data na gigabit kwara daya zai koma naira 431.25.
Da yake suka kan matakin, Ogunbanjo ya nemi masu amfani da layukan sadarwa da su yi tir da kin amincewa da karin, inda yake cewa masu amfani da layukan sun amince a yi karin kaso 5 ko 19 kacal ba wai kaso 50 da NCC ta sanar ba.
Ya lura kan cewa masu amfani da layukan sadarwar sun amince da su gurfanar da gwamnatin tarayya a kotu bisa amincewa da ta yi da karin kaso 50 na caje-cajen kamfanonin sadarwa.
Ogunbanjo ya koka kan cewa karin zai kara jefa jama’a cikin matsin rayuwa da suke fama da shi sakamakon janye tallafin mai wanda ya janyo tashin farashin sufuri da kayan abinci, wanda ya kai kaso 38.90 a watan Disamban 2024.
“Abun takaici ne sanarwar da karin farashin kiran waya da na data da minista ya yi, kuma za mu je kotu mu kalubalanci wannan amincewar karin kaso 50 da gwamnatin tarayya ya yi domin mu mun amince da karin kaso 5 ko 10 kacal ne. Su kamfanonin sadarwar kudi kawai suke son yi a kan masu amfani da layukansu,” ya koka.
Shi kuma jami’in yada labarai na kungiyar masu mu’amala da kudade ta wayar tarho da wakilansu na bankuna a Nijeriya, Ogungbayi Ganiyu, ya ce, mambobinsu ba su da wani zabi illa su kara kudin cajin da suke yi wa jama’a.
Ya ce, mambobin suna tsakamai wuya, musamman ta fuskanci sayar da data, kuma tilas jama’a su ga sauyi bisa wannan karin da NCC ta amince da shi.
Daga nan ya ce jami’an da ke sarrafa PoS da yiwuwar su kara kudin cajin da suke yi domin hakan ne ya zama musu dole.
Karin kudin kira da na data da sauran cajin kamfanonin sadarwar ana tunanin zai fara aiki ne daga watan Fabrairun 2025, ya zama wani karin tsarin manufar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ke kara janyo matsin rayuwa ga al’umma.
A kwanakin baya ne dai kamfanonin sadarwar suka yi barazanar cewa muddin ba a amince musu da karin kudin da suka tatsar jama’a ba, to tabbas za su rufe ayyukansu a Nijeriya.