Ofishin kula da aikin binciken sararin samaniya na kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati na kasar Sin ya bayyana cewa, ofishin ba da umurni na ayyukan kumbon binciken sararin samaniya na kasar Sin, ya tsaida kuduri cewa, ‘yan jannati uku wato Fei Junlong, da Deng Qingming, da Zhang Lu za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15, karkashin jagorancin Fei Junlong.
Gobe Talata ne, za a harba kumbon Shenzhou-15 cikin sararin samaniya daga cibiyar harbar kumbona ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp