Da safiyar yau Litinin ne ‘yan sama jannatin kasar Sin 3, na kumbon Shenzhou-18, suka iso doron duniya lami lafiya bayan gudanar da ayyukan watanni 6. ‘Yan sama jannatin Ye Guangfu, da Li Cong da Li Guangsu, sun sauka da karfe 1 da mintuna 24 bisa agogon birnin Beijing, a tashar saukar kumbuna ta Dongfeng dake jihar Mongolia ta gida a arewacin kasar Sin.
Bayan saukarsu, sun kuma bar cikin sundukin da ya dawo da su doron duniya da karfe 2 da mintuna 15, kamar dai yadda hukumar lura da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA ta bayyana.
- Tinubu Ya Himmatu Wajen Rage Raɗaɗin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki, In Ji Minista
- Ƴansanda Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje 130, Da Ake Zargi Da Sata Ta Yanar Gizo
Kafin dawowar su doron duniya, ‘yan sama jannatin 3, sun shafe tsawon kwanaki 192 a sararin samaniya, kuma hukumar CMSA ta ce sun kammala dukkanin ayyukan da aka tsara za su gudanar tare da kumbon Shenzhou-18 cikin nasara.
A ranar 25 ga watan Afililun shekarar 2024 ne kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Shenzhou-18 dauke da ‘yan sama jannatin su 3. Kuma yayin aikin su, sun gudanar da gwaje gwajen kimiyya a sassan kumbon, da amfani da na’urorin dakon samfura wajen aiwatar da gwaje gwaje masu tarin yawa.
Kaza lika, ‘yan sama jannatin na Shenzhou-18 sun gudanar da aikin daukar samfura a wajen kumbon su har sau biyu. Har ila yau, sun kafa tarihin yin tattaki a watan Mayu, wanda ya zamo irin sa na farko mafi tsayi da ‘yan sama jannatin kasar Sin suka gudanar a tarihi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)