Da karfe 12:16 na safiyar yau Juma’a bisa agogon Beijing ne ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-15 na kasar Sin, suka kammala tattakin farko a wajen tashar binciken samaniya ta Sin.
Hukumar dake kula da ayyukan sama jannati ta Sin ko CMSA, ta ce yayin tattakin, ’yan sama jannatin sun gudanar da ayyuka daban daban, da tallafin wasu hannuwan mutum-mutumin inji.
Ana sa ran ’yan sama jannatin za su gudanar da karin tattaki a nan gaba, domin tantance ingancin fasahohin da aka tanada. (Saminu Alhassan)