‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 na kasar Sin sun kammala mika ragamar aiki na zagayen da’ira a sararin samaniya ga takwarorinsu na kumbon Shenzhou-21, inda ake sa ran za su dawo doron kasa a gobe Laraba 5 ga watan Nuwamba.
‘Yan sama jannatin rukunoni biyu sun gudanar da bikin mika mabudan tashar sararin samaniya ta kasar Sin a yau Talata.
Zuwa yanzu, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 su uku da suka hada da Chen Dong, Chen Zhongrui da Wang Jie, sun kammala dukkan ayyukan da aka tsara, kuma sun kimtsa tsaf domin saukowa kasa a sashen saukar kumbuna na Dongfeng da ke yankin jihar Mongolia ta cikin gida mai cin gashin kanta a arewacin kasar Sin.
A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














