‘Yan sama jannatin kasar Sin na kumbon Shenzhou-17 dake aiki a tashar binciken samaniya ta Sin, sun kammala mika aiki ga tawagar ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18, ana kuma sa ran za su dawo doron duniya a ranar Talata 30 ga watan nan na Afirilu.
A yau Lahadi ne tawagar ‘yan sama jannatin Shenzhou-17, suka mika makullan tashar binciken ta Sin ga takwarorin su na Shenzhou-18, yayin bikin mika aiki da suka gudanar.
- Nijeriya Ta Kammala Bayar Da Horo Kan Fasahar Hada Magunguna
- Sharhi: Bukatar Sake Farfado Da Kiwon Tarwada A Nijeriya
A cewar hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin (CMSA), kawo yanzu, ‘yan sama jannatin Shenzhou-17 su uku, sun kammala dukkanin ayyukan da aka tsara za su gudanar. Kuma ana sa ran a ranar Talata za su sauko doron duniya a tashar Dongfeng dake jihar Mongolia ta gida wadda ke arewacin kasar Sin.
Kumbon Shenzhou-17, na dauke da ‘yan sama jannati Tang Hongbo, da Tang Shengjie da Jiang Xinlin. An kuma harba shi sararin samaniya ne zuwa tashar bincike ta kasar Sin, wato Tiangong tun a watan Oktoban bara, ya kuma kasance cikin falakinsa tsawon kusan rabin shekara.
Shi kuwa kumbon Shenzhou-18 mai dauke da ‘yan sama jannati Ye Guangfu, da Li Cong, da Li Guangsu, an harba shi ne a ranar 25 ga watan nan na Afirilu, zai kuma yi aiki na tsawon wasu watannin 6. (Mai fassara: Saminu Alhassan)