Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kama tare da tsare mutane biyu bisa zargin satar Ragon Layya.
LEADERSHIP ta labarto cewa, al’ummar musulmai za su fara shagulgulan bikin babbar sallah daga ranar Asabar mai zuwa kana ana yanka dabbobi musamman raguna a lokacin bikin.
- Ba Za Ta Sabu A Sake Zabar Musulmai 2 A Kaduna Ba -SOKAPU
- An Kashe Mutane Biyar, Fursunoni 879 Sun Tsere A Harin Gidan Yarin Kuje – Gwamnati
A sanarwar manema labarai da kakakin ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fitar, ya ce wadanda ake zargin su ne Adetunji Alagbe da kuma Opeyemi Ogunlokun, wadanda aka kama bisa sace Ragon wani mutum mai suna Sodiq Abolore da ke yankin Ogijo a jihar.
Ya ce, wadanda ake zargin sun shiga gidan Sodiq wajen karfe 3 na daren ranar Talata, inda suka saci Ragon layyarsa, kan hakan ne ya shigar korafi ga ‘yan sanda.
“Sodiq a lokacin da suke barci cikin dare, sun tashi kawai suka ga babu Ragon Layya da kudinsa ya kai N120,000.”
Ya ce a lokacin da mai Ragon ya farka ya shiga neman dabbarsa sai ya hango mutum uku suna kokarin tura ragon cikin wata mota kirar Mazda nan take ya ankarar da ‘yan sanda.
“An Kama biyu daga cikinsu, dayan kuma ya gudu. Mun kwato Ragon su kuma barayin suna tsare a hannunmu.”