Abokai, kwanan baya wani jirgin kasa dauke da sinadarai masu guba ya kaucewa layin dogo a garin Eastern Palastine na jihar Ohio, lamarin da ya gurbata muhallin wurin sakamakon yadda sashen kula da al’amuran gaggawa na wurin ya daidaita hadarin.
Rahotanni da dama na nuna cewa, wadannan abubuwa masu guba sun kawo illa ga lafiyar mazauna wurin da kewaye. Hukumar kula da albarkatun jihar ta bayyana a ran 14 ga wata cewa, sinadarai masu guba sun gurbata kananan koguna 4 a wuraren dake da nisan kilomita 7.5 da aukuwar lamarin, abin da ya yi sanadin mutuwar kifaye a kalla 3500.
Amma, kafofin yada labarai ba su mai da hankali sosai kan wannan hadari mai muni ba, har zuwa ran 13 ga wata, an fara ganin hotuna ko bidiyo da dama game da illar da hadarin ya kawowa wannan wuri a shafukan sada zumunta, da ma mummunan sakamakon da hakan ke iya haifarwa. Abin mamaki shi ne, a wannan rana kuma, ministan sufuri na kasar Pete Buttigieg ya yi ta cika baki game da manyan ababen more rayuwa da ake ginawa a Amurka, amma bai ce komai game da hadarin ba.
Ban da wannan kuma, a wani taron manema labarai da aka yi a ran 8 ga wata a jihar, an cafke wani dan jarida yayin da yake watsa labari kai tsaye bisa doka, da nufin hana jama’a sanin abin da ya faru.
Shin ko mazauna wuri ba su da iko sanin halin da suke ciki yanzu?
Abin bakin ciki shi ne, mai magana da yawun gwamnan jihar Dan Tierney ya gayawa manema labarai a ran 16 ga wata cewa, wannan hadari ba bala’i ne daga indallahi, don haka jihar ta Ohio ta kasa samun agaji daga hukumar kula da halin ko ta kwana ta tarayyar Amurka, abin da al’ummar wurin suke matukar bukata don fita daga illar iska mai guba.
Jama’a na fama da kalubale na lafiya, amma ‘yan siyasa ba su dauki matakin da ya dace ba, inda suke kokarin boye halin da ake ciki. Muna iya cewa, wadannan ‘yan siyasa sun fi iska mai guba hadari.
Abin da suke sanya a gaba shi ne kokarin kiyaye moriyarsu ta siyasa kawai, sun toshe idanu da kunnuwansu game da kalubalen da jama’a ke fuskanta, kuma tsarin bayar da agaji, ya jefa wadannan mutane da hadarin ya shafa cikin mawuyacin hali, saboda bai damu da hakkinsu ba ko kadan. (Mai zana da rubuta:MINA)