Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin ta magance ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ke addabi al’ummar Nijeriya.
Buhari ya ce ‘”yan ta’adda da ‘yan bindiga ba rauhane ba ne, su ma mutane ne da ke zaune a cikin al’ummominmu.”
Don haka, dole ne sojoji su murkushe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron hadin kan kasa, zaman lafiya da tsaro da cibiyar hulda da jama’a da abokan hulda ta Nijeriya ta shirya, mai taken “Tattaunawa don sake gina Gaskiya da aminci”
“Idan aka yi la’akari da rahotannin da ake samu da kuma labaran da suka fara fitowa a cikin ‘yan kwanakin nan, zan ce lalle jami’an mu sun ji kokenmu. A cikin kwanakin da suka gabata, tabbas kun ji labarin adadin ‘yan ta’adda da sojoji suka kashe, da kuma adadin wadanda aka Kubutar daga hannun masu garkuwa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp