Akalla sojoji uku ne suka mutu yayin da wasu uku ciki har da wani Kwamandan Birget suka samu raunuka a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a wani sansanin sojoji na ‘Forward Operating Base’ (FOB) da ke Wajiroko a jihar Borno.
A cewar wata majiyar soji, kwamandan birget din ya samu rauni ne a lokacin da motar sa ta taka Bam da aka dasa kan hanyar zuwa wurin domin bayar da agajin gaggawa ga sansanin da aka kai wa harin.
- Sin Ta Samu Bunkasa A Fannin Neman Ikon Mallakar Fasaha A Ofishin EPO
- Kantoman Ribas Ya Naɗa Farfesa Lucky Worika A Matsayin Sakataren Gwamnati
Majiyar ta ce, da misalin karfe 10:05 na daren ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025, Boko Haram/ISWAP sun afka wa rundunar soji ta FOB da ke Wajiroko.
Hakan ya sa, rundunar FOB ta yi kira da akawo musu dauki ta sama baya ga aikewa da karin tawaga ta kasa domin tallafawa. Duk da haka, tawagar ta sake cin karo da Bam a kan hanya.
Duk da cewa, ba a samu cikakken bayanin harin ba a lokacin rubuta wannan rahoton, amma an samu cewa, matukin jirgin yakin da aka aika domin bayar da agaji ta sama, ya sanar da cewa, yana iya hango wuta tana ta shi a kusa da FOB sannan wasu sojoji da dama na gudu zuwa Sabon Gari, kamar dai, an riga an kwace sansanin FOB din.”
Darakta, Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, bai amsa sakon da Wakilinmu ya aika masa ba domin tabbatarwa a lokacin fitar da wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp