Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa, ta tabbatar da wani hari da ‘yan ta’adda suka kai wa al’ummar Kwapre a Karamar Hukumar Hong a ranar Kirsimeti.Â
Kakakin ‘yansandan, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) lamarin a Yola a ranar Talata.
- An Kashe Mutane 700, An Lalata Kauyuka 50 Cikin Wata 3 A Mazabata — Sanata
- Sojojin Faransa Sun Kammala Ficewa Daga Nijar Gaba Daya
Ya bayyana cewa tuni aka fara gudanar da bincike kan harin.
A cewar Nguroje, Kwamishinan ‘yansanda Babatola Afolabi ya tura jami’an ‘yansanda zuwa wurin da lamarin ya faru tare da ba da umarnin gudanar da cikakken bincike.
Ya kuma bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani da ba a yarda da shi ba ga hukumomin tsaro don inganta tsaro a jihar da kasa.
Shugaban gundumar Dugwaba, Mista Simon Buba, ya kuma tabbatar wa manema labarai cewa mutane biyu sun mutu yayin harin.
Ya kara da cewa maharan, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun isa yankin a kan babura, sannan suka sace kayan abinci suka kuma gudu zuwa dajin Sambisa.