Kimanin sa’o’i 24 da ‘yan ta’adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El’Rufai a wani faifan bidiyo, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa sojojin Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.
Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya cikin firgici.
A wani rahoton da the Nation ta bayar, ta ce ‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon shari’a ta Nijeriya da ke Bwari ne a lokacin da suka ci karo da sojojin suna sintiri.
Akwai rahotannin sirri, kamar yadda majiyar sojoji ta bayyana, ‘yan ta’addan sun mamaye babban birnin tarayya, Abuja da nufin kai hari a makarantar koyon aikin Shari’a da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati.
Majiyoyin soji da suka nemi a sakaya sunansu sun ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin amma hukumomi sun ce suna kan bibiyan sahun maharan.
A cewar daya daga cikin majiyoyin, yace ‘yan ta’addan sun yi wa dakarun rundunar bataliya ta 7 dake sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna ne.
Ya kara da cewa sojoji uku ne suka jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibitin THE domin kula da lafiyarsu.