Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Garba Muhammad, ya ce ‘yan ta’adda sun yi barazanar sanya bam a ginin Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja.
Garba, ya bayyana hakan ne yayin wani taron sauraron ra’ayoyi kan ƙudirin da ke neman kafa Hukumar Tsaron Majalisar Dokoki domin inganta wa ‘yan majalisar, ma’aikata da baƙi da ke shiga majalisar tsaro.
Ya ce majalisar ta fuskanci matsaloli da dama na tsaro, ciki har da satar motoci da babura, lalata kayayyaki, amfani da katin shaidar ƙarya, da kuma shigowar baƙi da ba su da rijista.
Garba ya gargaɗi cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, lamarin na iya zama barazana ga ayyukan majalisar.
“Mun samu barazanar ‘yan ta’adda da ke shirin tarwatsa ginin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, da kuma masu zanga-zanga da ke shirin rufe majalisar,” in ji shi.
“’Yan majalisa suna kuma fuskantar barazana daga wasu ‘yan yankunansu da ke samun damar shiga ofisoshinsu ba tare da izini ba.”
Ya ƙara da cewa idan aka kasa magance waɗannan matsalolin tsaro, hakan na iya kawo cikas ga gudanar da ayyukan majalisar kamar wakilci, sa ido, tattaunawar kasafin kuɗi da zaman majalisar, wanda zai iya shafar tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.
A watan Mayun shekarar 2021 ma, an taɓa samun irin wannan gargaɗi lokacin da Boko Haram ta yi shirin kai hari Majalisar Dokoki da wasu muhimman gine-ginen gwamnati a Abuja.
Bayan wannan gargaɗi, an taƙaita shiga majalisar, inda masana tsaro suka buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara tsaurara matakan tsaro a muhimman wuraren gwamnati.
Garba, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da tsaron Majalisar Dokoki kafin wani abu ya faru.














