‘Yan takarar gwamna bakwai a zaben gwamnan jihar Kaduna da ke tafe a ranar 11 ga Maris, 2023, sun amince su marawa dan takarar jam’iyyar PDP, Rt. Hon. Isah Muhammad Ashiru Kudan baya.
‘Yan takarar gwamnan sun hada da na jam’iyyun YPP, AA, APM, APP, APGA, NRM, da ZLP.
- Zaben Gwamna: Zan Shawo Kan Matsalar Rashin Aikin Yi A Jihar Kebbi – Aminu Bande
- Timi Frank Ya Bukaci Shugaban INEC, Yakubu, Ya Yi Murabus
Masu neman takarar gwamnan sun bayyaa haka lokacin da suke zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar, Ambasada Sanin Yaya, ya ce bayan tattaunawa da mambobinsu da magoya bayansu a fadin Jihar, sun yanke shawarar hada karfi da karfe da dan takarar PDP don fatattakar Jam’iyyar APC da ta addabi al’ummar Kaduna.