• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Wasa Biyar Da Suka Taka Rawar Gani A Kofin Zakarun Turai

by Abubakar Abba and Sulaiman
4 months ago
UEFA

Za a iya cewa mabiya harkar wasanni kalilan ne – idan ma akwai – suka yi hasashen kungiyar Paris Saint-Germain za ta lashe gasar zakarun Turai ta Champions League da aka kammala kafin fara ta. PSG ta cinye Inter Milan 5-0 a binrin Munich na Jamus a wasan karshe, wanda masana suka ce shi ne wasan karshe na farko da wata kungiya ɗaya ta fi mamaye wasan a tarihi.

Wannan ne karon farko da PSG ta lashe gasar, kuma ta biyu da ta yi hakan daga kasar Faransa. Kakar ta shekarar 2024 zuwa 2025 ta zo da abubuwa da dama, ciki har da sabon salon buga wasannin rukuni, da kuma kara yawan tawagogin da ke shiga gasar daga 32 zuwa 36.

Ousmane Dembélé

Danwasan gaba na Paris Saint-Germain, Ousmane Dembélé, shi ne hukumar kwallon kafa ta Turai Euefa ta zaba a matsayin mafi hazaka a gasar ta Champions League. Demebele ya kai matsayin ne saboda irin taimakon da ya bai wa zakarun na Faransa ta hanyar jefa kwallaye takwas a raga, da kuma bayar da gudummawar cin wasu shida a wasa 15 da ya buga a gasar ta zakarun turai.

LABARAI MASU NASABA

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23.

Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45.

Rapinha

Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai. Tare da dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan kwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da kwallo a zira a raga, inda yake da guda 9, Guirassy ke da 4.

Rapinha mai shekara 28 ya ci ƙwallo tara da ƙafarsa ta hagu, uku da dama, da kuma ɗaya da kansa. Huɗu daga cikin ƙwallayen da ya ci daga wajen yadi na 18 ne.

Wani abu da ya kamata a lura da shi shi ne babu bugun finareti ko ɗaya cikin ƙwallayen da ya ci a wasa 14 da ya buga.

Lamine Yamal

Duniya ta fara maganar dan wasa kuma matashin da ya fi birge ‘yankallo ko shakka babu shi ne Lamine Yamal na Barcelona. Dan wasan na Sifaniyan mai shekara 17 ya taka rawar gani cikin wasanni 13 da hya buga wa kungiyar, inda ya kai hare-hare har sau 52. Daga cikinsu akwai munana 25. Yamal ya ci kwallo biyar sannan ya bayar da uku aka zira a raga. Sannan ya yi nasarar yanka abokan hamayya har sau 109 a gasar, wadda ita ce ta biyu da ya buga wa Barcelona.

Serhou Guirassy

Shima dan wasa Serhou Guirassy wani danwasan da ya taka rawar gani a kakar da aka kammala shi ne Serhou Guirassy na Burossia Dortmund da kuma Faransa. Danwasan mai shekara 29 ya jefa kwallaye har 13 a raga – iri daya da na Rapinha – sannan ya bayar gudummawa aka ci wasu hudu cikin wasa 14. Cikin kwallayen da ya ci har da uku rigis ya dura wa Barcelona a wasa na biyu na zagayen kusa da na kusa da na karshe.

Harry Kane

Danwasan gaba na Bayern Munich kuma kyaftin ɗin Ingila ya ɗora kan abin da ya saba, inda bai gushe ba sai da ya zira kwallaye 11 cikin wasanni 13 da ya buga wa kungiyar, kazalika, Kane mai shekara 31 ya kai hare-hare 49, cikinsu akwai masu hadari 25. Haka nan, ya bayar da kwallo biyu an zira a raga kafin Inter Milan ta yi waje da su daga gasar a zagayen kusa da na karshe.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid
Wasanni

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru
Wasanni

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Next Post
Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

LABARAI MASU NASABA

Turai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.