Kofin Duniya na FIFA na 2026, wanda za a buga a kasashen Kanada, Amurka da Mexico, zai zama gasa mai tarihi, ba wai kawai saboda zai zama bugu na farko da ƙasashe 48 za su halarta ba, har ma saboda zai iya zama wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ga wasu manyan ‘yan wasa a shekaru 15 da suka gabata.
‘Yan wasan ga su haka:
1.CristianoRonaldo (Portugal)
2.LionelMessi (Argentina)
3.LukaModrić (Croatia)
4.ManuelNeuer (Jamus)
5.VirgilvanDijk (Netherlands)
6.HarryKane (Ingila)
7. RobertLewandowski (Poland)
8.SonHeung‑min (Koriya ta Kudu)
9.MohamedSalah (Masar)
10.Luis Suárez (Uruguay)
Tasirinsu a kungiyoyi da ƙasa na da matukar muhimmanci, kuma 2026 na iya zama damarsu ta ƙarshe ta haskakawa a babban kofin ƙwallon ƙafa mafi daraja.
Biyu da suka yi fice acikin 10, sun hada da Cristiano Ronaldo (Portugal). Yana da shekaru 41, ya tabbatar da cewa wannan zai zama gasarsa ta ƙarshe, yana da niyyar ƙara Kofin Duniya a cikin jerin kofunan da ya taɓa lashewa.
LionelMessi (Argentina).
Bayan ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2022, ɗan wasan mai shekaru 39 ya nuna cewa gasar 2026 a Arewacin Amurka na iya zama damarsa ta ƙarshe don kare kambun.
…rahoto daga Tribune














