Bayan kammala wasannin kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 a ranar Laraba, zamu lissafo ‘yan wasan da ke kan gaba wajen zura kwallaye a gasar ta Qatar.
Morocco tayi rashin nasara a hannun Faransa da ci 2-0 a daren Laraba inda ta samu tikitin shiga wasan karshe, yayin da Argentina ta doke Croatia da ci 3-0 a ranar Talata.
Kaftin din Argentina Lionel Messi a halin yanzu ya kamo dan wasan gaba na Faransa, Kylian Mbappe, a gasar cin kofin duniya da ke gudana da kwallaye biyar kowannensu.
Bayan Messi da Mbappe akwai Julián Álvarez na Argentina da Olivier Giroud na Faransa.
Ga ‘yan wasan da suka fi zura kwallaye a gasar cin kofin duniya kafin karawar karshe tsakanin Faransa da Argentina a ranar Lahadi:
Kwallaye 5: Lionel Messi da Kylian Mbappe
kwallaye 4: Olivier Giroud da Julián Álvarez.
kwallaye 3: Marcus Rashford, Bukayo Saka, Cody Gakpo, Alvaro Morata, Richarlison, Gonçalo Ramos da Enner Valencia.
Kwallaye biyu: Mohammed Kudus, Ritsu Doan, Mehdi Taremi, Vincent Aboubakar, Giorgian de Arrascaeta, Robert Lewandowski, Neymar, Ferran Torres, Rafael Leão, Kai Havertz, Harry Kane, Niclas Fullkrug, Bruno Fernandes, da Wout Weghorst.