A ci gaba da kawo muku hirar da Wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood, kuma Jarumi mai taka rawa a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa24, wanda ya shafe shekaru sha biyar a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, MUHAMMADU MURTALA wanda aka fi sani da DANTANI MAI SHAYI.a wanann makon ya tabo bangarori da dama na rayuarsa a a masana’antar kannywood, musamman irin burin a nan gaba, gad ai yadda hirar ta kasance:
Wanne irin Nasarori ka samu game da fim?
Alhamdulillahi mun mallaki abubuwa da dama a wannan masmana’antar, kuma an yi sutura an taimaki ‘yan uwanka, an taimaki wani ma wanda ba dan uwanka ba, kuma ka mallaki gida, ka mallaki abubuwa da sauransu. Rufin asiru dai Alhamdulillahi harkar ta rufa mana asiri ba abin da za mu ce da Allah sai dai mu kara gode masa.
Me ka ke son cimma game da fim?
Abin da nake son cimma shi ne; a kulli yaumin mu rinka fadakar da mutane masu laifi su daina.
Bayan harkar fim, kana wata sana’ar ne?
Eh! Ina yi, ina harkar kasuwanci na Shaddodi da Atamfofi.
Ya kake iya hada kasuwancinka da kuma harkar fim dinka?
Kasuwanci daban, harkar fim d ban, saboda ‘Online Business’ nake.
Ko kana da ubangida a cikin masana’antar?
Eh! Ina da Ubangida, Ali Jita shi ne Ubangidana a masana’antar.
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Suna da yawa irinsu; Kansila, su Mai Nasara, Kabiru Makaho, su Sajen Bala, su ‘Yar Auta, suna da yawa gaskiya.
Da wa ka fi so a hada ka a fim, kamar bangaren iyaye da kuma matasa?
Bangaren fim ina so a hada ni da Bosho, ina jin dadin aiki da shi ko Nuhu Kansila, a matasa kuma kowa ma a hada ni da shi.
Misali kamar su; Ali Nuhu, Adam Zango, Gabon da sauransu.
Eh! Su ana mutunci sosai kuma muna fim da su, akwai wani fim ma da muka yi da Ali Nuhu muka yi na fito a maigadinsa, Hadiza Gabon kuma kamar wani fim dana fada miki BABBAN ZAURE kusan shi ne fim dinta na farko shi ma ina cikin wannan fim din, Adamu Zango sosai mutumina ne, yana ba mu shawara sosai Adamu, akan mu ruke harkar da muke da mutunci, wadannan suna ba mu shawara ta gari
Ka taba yin dariya a lokacin da ake tsaka da daukar fim ba tare da ka sani ba?
Akwai wanda kuna tsakiyar yi ma dariya za ta kufce, ku da kanku za ku bawa kanku dariya, ku kwace da dariya sai a dakatar a sake daukar wani, dole ne daman ana dauka dole sai ka yi dariya, ana yi.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai, na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ka taba iya mantawa da shi a rayuwa ba?
Toh! abin da ya taba faruwa da ni na farin ciki wanda ba zan taba mantawa da shi ba shi ne; Lokacin da aure na ya taso a masana’antar nan abin da aka yi mun shi ba zan taba mantawa ba, an nuna mun da ne ni, an yi mun kara, kusan komai wajen ‘Dinner’ Ali Jita duk shi yayi, to na ji dadin wannan. Sai abu na biyu kuma a wannan sana’ar mun taba zuwa mun yi dirama gaban wasu gwamnoni guda uku, kowanne ya ba mu mota, ba zan taba mantawa da wannan ba, sannan kuma duk wajen da muka je manyan mutane yadda suke nuna mana karamci da mutunci shi ma ina jin dadinsa a rayuwata.
Matar da ka aura ita ma ‘yar fim ce?
Mata ta ba ‘yar fim ba ce.
Za mi ci gaba a mako mai zuwa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp