Masu karatu assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata muna kan darasi ne a game da abubuwa na al’adar rayuwa da yanayin yadda Annabi Muhammadu SAW yake nasa. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya inda a yau darasin zai fi mayar da hankali a kan yanayin cin abinci da baccin Annabi SAW.
Sayyidina Aliyu (Karramallahu Wajhahu) yana cewa, duk wanda ya yi bacci har na tsawon Sa’o’i Uku, to ya biya abin da ya wajaba a kanshi. Larabawa da duk masu hikima na daga Malaman falsafa da likitanci, sun tafi a kan cewa, yana da kyau a karanta cin abinci da bacci. Kamar yadda yakan zama zargi ga mutane na kabilu daban-daban a ce “wa ne ya cika cin abinci”. Babu wani da yake alfahari a ce masa ya cika cin abinci.
- Tashar Samar Da Wutar Lantarkin Nijeriya Ta Sake Lalacewa A Karo Na 11
- Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Fa’idojin CIIE Na Ci Gaba Da Karuwa
Amma fa duk da haka, ana nufin karanta cin abinci yadda ba zai illata mutum ba. Domin yawaita cin abinci da shaye-shayen kayayyaki, yana nuni da cewa, mutum yana da zari da handama. Allah Ubangiji ya ce “Kulu washrabu wala tusrifu” ku ci abinci ku sha ruwa amma kar ku yi barna (Malamai sun ce duk kiwon lafiya yana cikin wannan ayar).
Yawaita cin abinci yana jawo cutar Duniya da Lahira: cutar Duniya, Ita ce: idan ka kashe Naira N5,000 wurin cin abincin hadama, to akwai yiwuwar kashe ninkin abin da ka kashe wurin cin abincin hadama don neman lafiya, misalin irin su ciwon Siga, Ulcer da dai sauransu. Cutar Lahira, ita ce: Mutum ba zai yi kuzari ba wajen yin Ibada, sabida cututtukan gabobi za su tunkaro masa. Ana cewa, kyawun namiji in ya bi abu (kamar farautar dabbobi) to ya kama abun, amma in shi ne ya tsare ma abun to kar abun ya cimma sa. Haka Larabawa suke gwada namiji.
Akwai wasu mutane da suke gwada hankalin mutum da amfani da tsakuwa: suna zuwa wajen mutum ne yayin da yake bacci sai a jefa masa tsakuwar a gani ko zai farka, in ya farka to ya yi hankali, in bai farka ba to akwai bukatar a sake kula da hankalinsa.
Sai dai, galibi masu karanta abinci, za ka same su suna shan kayan itatuwa wanda zai taimaka ma jininsu bugawa. Amma karanta abinci da bacci yana nuni da cewa mutum yana da wadatar zuciya, sabida yakan iya kula da tsarin jikinsa, sannan kuma karanta abinci da bacci yana tumbuke sha’awa. Sakamakon hakan, sai ya kara wa mutum lafiya da karfin tunani da kaifin hankali.
Yawaita bacci, yana nuni da alamar mutum mai kasala ne, yana kawo karancin fahimta da kaifin tunani sannan kuma zai tozarta rayuwarsa a kan bacci da mutuwar zuciya. Wannan karatu ne da kowa ya san shi a al’ada, don haka, ba a bukatar hujjar aya ko hadisi.
Saboda haka, duk wanda ya karanta ko ya yawaita bacci sai an ga wadannan siffofin da muka lissafa. Amma kuma duk da haka, akwai maganganun mutane masu hikima da maganganun al’ummatai daban-daban da wakokin larabawa da hadisan Annabi Muhammad SAW da suke tabbatar da wadannan hikimomin.
Don haka, duk tarihin Annabi SAW za kaji yana karanta bacci da cin abinci. Akwai hadisi da aka ruwaito Annabi SAW ya jera kwanaki Uku yana azumi, “Ba Sahur ba buda baki” Sahabbai za su yi ya ce musu, A’a “ni ina kwana wurin Ubangijina, yana ciyar da ni kuma yana shayar dani”, haka kuma, in ka ji tarihin rayuwar Annabi SAW kan yadda yake bacci, abu ne da hankali ba zai fahimta ba.
An karbo hadisi daga mikdahi, ya ce, Annabi SAW ya ce, “Dan Adam bai cika wata jaka ko kwarya ba, mafi muni irin cikinsa”. Ya ishi dan Adam daga cin abinci na wasu ‘yan lomomi – Na Safe, Rana da dare. In mutum ba zai iya yin ‘yan lomomi ba, to, masu hikima suka ce ya raba cikinsa gida Uku: bangaren Abinci da Ruwa da Numfashi.
Malam Sufyanus Sauri, yana cewa: da karanta abinci ake mallakar bacci a dare, amma in ciki ya cika babu abin da zai rage, sai bacci.
Wasu bangare daga cikin magabata, sun ce, “Kar ku ci abinci da yawa, sai ku yi ta bacci da yawa, sai kuma ku yi asara da yawa (Babu Ibada ballantana Zikiri).
An ruwaito daga Annabi SAW cewa “Mafi soyuwar abinci a wurin Annabi SAW shi ne, wanda aka ci a cikin taro, hannaye suka yi yawa cikin abincin”.
An ruwaito daga Sayyada A’isha Ummil Mu’uminina tana cewa, “cikin Annabi bai taba cika ba da dai,” Manzon Allah SAW ya kasance a cikin Iyalinsa bai tambayar abinci, abin da aka ciyar da shi sai ya karba, haka ma abin da aka shayar da shi sai ya karba”.
Rayuwar Annabi Muhammmad SAW sabanin tamu ce, abin da Allah ya ba shi na hadiyya daga Mutane, sai ya bai wa kowacce daga cikin Matansa, abincin Shekara.
Karanta abinci, kowa da irin zuhudunsa, kar ka matsa wa iyalinka dole sun bi irin zuhudunka.
Ma’ana: Abin da hadisin yake nufi shi ne, Annabi SAW yana baiwa matansa kowacce abincin shekara, sabida haka abincin ya zama nata, ta yi yadda take so da shi, to duk abin da ta yi ta ba shi sai ya karba sabida nata ne shi kuma ba shi aka yi.
Akwai wani hadisi na Barira ‘yar aikin daya daga cikin matan Annabi ce, SAW, wata rana an ba ta sadakar mama, ta sa a wuta tana dafawa, sai Annabi SAW ya zo wucewa sai ya gani ana dafa nama, bayan kai masa abinci sai bai ga an sa masa nama ba (Annabi SAW ya san iyalinsa ba za su samu abu su hana shi ba), sai Matarsa ta ce ya Rasulallahi, Sadaka ce aka bai wa Barira, mu kuma ba ma cin Sadaka, sai Annabi SAW ya mayar mata da amsa cewa, Barira nata Sadaka ce, ni kuma ta ba ni kyauta.
Da irin wannan ne malamai suka yanke hukuncin cewa, in ba ka cin sadaka, sai aka bai wa wani, shi kuma ya kai ma wanda ba ya cin Sadaka, to ya amsa, shi a wurinsa yanzun, kyauta ce.
Yana daga darajar aure, mata ba ta tuhumar mijinta a kan abin da ya ba ta, shi ma baya tuhumar matarshi a kan abin da ta bashi. Sabida dukkansu sun san akwai soyayya da rahama a zuciyarsu. Da wani abin jarrabawa zai taso, da a baya zai sa su sai abin ya fara gamawa da shi tukunna kafin ya isa wurinsu.
Yazo daga cikin hikimomin Lukmanal hakimu: “In ka cika cikinka, sai hankalinka ya yi bacci, ba za ka iya tunani ba, sai gabbai su kasa yin Ibada”
Akwai wani almajirin Imam Malik yana cewa “Ka bar wa Malamai Ilimi in ba za ka karanta cin abinci ba”.
Ya zo a cikin hadisi, Annabi SAW yana cewa, “Ni ba na cin abinci ina kishingide” abin da Malamai suka fassara da shingida a nan shi ne, Zaman dirshan don cin abinci, yana ba wa mai cin abincin damar cin abinci mai yawa, sabida tsari da yanayin zaman yana ba wa mai zaman damar cin abinci sosai.
Manzon Allah SAW yana cewa: “innama ana abdun, a’akulu kama ya’a kulul abdu wa’ajlisu kama yajlisu”, ni bawa ne, ina cin abinci kamar yadda bawa ke ci, kuma ina zama kamar yadda yake zama” a wannan hadisin, yana nufin ba zaman a kishingida ba, a’a zama kamar irin na takama.
Haka baccin Annabi SAW ya kasance kadan ne, kuma a gefen hannun dama yake kwanciya. Bacci a gefen dama ba ya nauyi, ba wuya mutum ya farka, sabida zuciya tana gefen hakarkari na dama, ma’ana a wannan yanayin baccin zuciya tana sama, amma in ka kwanta a bangaren hagu, ka danne ta, don haka bacci zai yi nauyi.
Duk hadisai ingatattu da aka ruwaito sun tabbatar da karanta baccin Annabi SAW. Kuma duk da cewa baccin kadan ne amma sai ga Hadisi yana cewa: “inna ainaiya tanamani, wala yanamu kalbi”, idanuna ce kadai take bacci amma zuciyata ba ta bacci.
Amma mu kuma, mu yi bacci ba mu jin komai, shi ne mun yi bacci. Da yawa za ka ji mai bacci yana cewa masu surutu kusa da kaina duk sun hana ni yin bacci, kuma duk da cewa ya kulle idanuwansa, amma SAW ya ce shi hakan shi ne baccinshi.