A ranar 29 ga wata, aka cika kwanaki 100 da gwamnatin kasar Amurka karkashin jagorancin Donald Trump ta kama mulkin kasa, amma a maimakon yabo da gamsuwa, suka kawai take sha daga ciki da wajen kasar.
Binciken da kafofin yada labarun Amurka suka gudanar cikin hadin gwiwa a kwanan baya ya nuna cewa, wadanda suka shiga binciken da yawansu ya kai 55% ba su amince da yadda gwamnatin Trump ke mulkin kasar ba, adadin da ya zama na farko cikin shekaru 80 da suka wuce.
- Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
- Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis A Matsayin Hutu
Sallamar dimbin ma’aikatan gwamnatin tarayya, daidaita batun baki ba ta hanyar da ta dace ba, rage makudan kudade kan harkokin nazarin kimiyya, aiwatar da manufar ramuwar haraji kan dukkan abokan ciniki da sauran manufofi da matakai da gwamnatin Trump ta dauka sun yi mummunan tasiri kan al’ummar Amurka da tattalin arzikin kasar. Mujallar Nature ta gabatar da sakamakon bincikenta cewa, masu nazarin kimiyya na Amurka da yawansu ya kai 75% suna duba yuwuwar barin kasar.
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.
Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai EU ta zartas da matakan mayar da martani kan Amurka a zagaye na farko. Firaministan kasar Japan Ishiba Shigeru kuma ya bayyana a fili cewa, bai shirya mika wuya don cimma yarjejeniya kan harajin kwastam cikin hanzari ba.
Yanayin rudani da Amurka ke ciki cikin kwanaki 100 da suka gabata ya ilmantar da jama’a cewa, babu wanda zai yi danniya bisa ganin dama. Kuma babu wanda zai hana dunkulewar tattalin arzikin duniya. Hadin gwiwa mai kunshe da kowa da samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare, ita ce hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp