Ofishin Akanta Janar na Tarayyar Nijeriya ya gano manyan koma-baya ga aiwatar da hukuncin koli na ranar 11 ga Yuli, 2024 kan cin gashin kan kananan hukumomi, inda ta ce kananan hukumomin 749 sun gaza bayar da bayar da cikakkun bayanan asusunsu.
A cewar hukumar gwamnatin, manyan koma-baya guda biyu ne suka hana kananan hukumomin sumun ‘yancin kai, wadanda suka hada da rashin mika cikakkun bayanan asusun, inda ta kara da cewa da tantance kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, ya zama wajibi su karbi kudadensu kai tsaye.
- Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
- Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar Zamfara
Wannan yana kunshe ne a cikin abubuwan da aka tattauna a taron kwamitin raba asusun tarayya, wanda aka gudanar da karshen mako.
Akanta janar ta tarayya, Oluwatoyin Madein ce ta jagoranci taron.
A halin da ake ciki dai, ofishin akanta janar da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a sun fara tattaunawa don magance koma-bayan da aka samu, a cewar majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin.
A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye.
“Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu.
“Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.”
Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba.
Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas.
“Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don tabbatar da cewa sun sami kasosu kai tsaye. Wannan ya faru ne saboda abubuwa da yawa na bukatar a magance su,” in ji ta.
Idan za a iya tunawa dai, Babban Bankin Nijeriya ya fara bayyana shugabanni da masu sa hannun a asusun bankuna na kananan hukumomi 774 da ke kasar a wani mataki na fara cin gashin kan kananan hukumomi.
Daraktan kula da harkokin shari’a na Babban Bankin Nijeriya, Kofo Salam-Alada, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin tabbatar da bin diddigin kudade.
“Wannan duk na cikin tsari sanin abokin hulda. Duk wanda zai zama mai sa hannu a asusun dole ne a bayyana shi.
“Tsarin yana ci gaba, kuma muna hadin gwiwa da ofishin akanta janar. Mun kuma rubuta wa kananan hukumomin,” inj i shi.
Sai dai kungiyar shugabnnin kananan hukumomin Nijeriya ta ce ba ta samu wata sanarwa daga babban bankin kasar ba dangane da bude asusun ajiyar banki.
Idan za a iya tunawa, a ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta tabbatar da ikon cin gashin kananan hukumomi 774 da ke kasar nan tare da haramta wa gwamnoni ci gaba da kula da kudaden da aka ware wa kananan hukumomi.
Kotun kolin ta kuma umurci Akanta Janar na Tarayya da ta biya kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusunsu, inda ta bayyana rashin fitar da kudaden da jihohi 36 suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Amma watanni takwas bayan yanke hukuncin, har yanzu ba a fara aiki da hukuncin cin gashin kan kananan hukumomi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp