Kakakin ofishin kula da harkokin HK da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata sanarwa a yau Lahadi, inda ya soki mataki na rashin sanin ya kamata da majalisar wakilan Amurka da kwamitin kula da harkokin kasar Sin suka dauka na kiran taron sauraron ra’ayi kan wasu rahotanni dake sukar dokokin tsaron kasa na HK da tsarin shari’ar yankin, tare da neman kakabawa wasu jami’an HK din takunkumi.
A cewar kakakin, ‘yancin da bangaren shari’a na HK ke da shi, ba zai bari Amurka ta rika tsoma baki cikin harkokin yankin ba, haka kuma gwamnatin tsakiya ta kasar Sin na goyon baya tare da bayar da tabbaci ga ‘yancin da rashin bangaranci a bangaren shari’ar da ma ma’aikatansa, wajen sauke nauyin ayyukan da suka rataya a wuyansu bisa doka.
Ya kara da cewa, ‘yancin bangaren shari’a abu ne da aka yi na’am da shi a dokokin kasa da kasa, kuma ‘yancin alkalai na gudanar da shari’a ba tare da an tsoma musu baki ba, muhimmiyar nasara ce ga tsarin shari’a.
Bugu da kari, ya ce ‘yan siyasar Amurka dake ikirarin daukaka dokoki da ‘yancin bangaren shari’a, suna neman kakaba takunkumai da yin barazana ga alkalai a yankin HK. Yana mai cewa, wannan ya keta tsarin dokokin kasa da kasa da tushen ka’idojin siyasa. (Mai fassarawa: Mustapha Fa’iza)