• Leadership Hausa
Monday, May 29, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

APC Ce Za Ta Yi Nasarar Samar Da Shugabanci A Majalisa – Hon. Wase

by Bashir Bello, Abuja
2 weeks ago
in Siyasa
0
APC Ce Za Ta Yi Nasarar Samar Da Shugabanci A Majalisa – Hon. Wase
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mataimakin kakakin Majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya a zauren Majalisa karo na tara, Honarabul Ahmed Idris Wase ya yi ikirarin cewa Jam’iyyarsu ta APC za ta yi nasara da rinjaye mai girma a zaben shugabancin majalisar ta 10 da za a rantsar.

Dan Majalisar mai wakiltar mazabar Wase ta Jihar Filato, kuma wanda ya kasance daya daga cikin yan takarar Kujerar shugabancin Majalisar wakilai a zauren Majalisar, ya bayyana hakan ne a wani zantawar sa da manema labarai a garin Abuja.

  • An Kashe Fitacciyar Mawaƙiyar Nan Ta Sudan Shaden Gardoodd

Idris Wase, ya kara da cewa a bisa shirye-shiryen da su ke, sun samu gabatar da taro na niyyar su ta neman shugabancin Majalisar Kasa na kujerar kakakin Majalisar wakilan tarayyar kasar kuma suna ganin sun kai gabar da ya kamata su fada wa mutane ‘yan Jam’iyyar su, masoya tare da magoya baya cewa lokaci ya kai.

“Duk da cewa akwai ‘yan Jam’iyyar adawa da su ma suke ganin za su iya hada kai su nema, ina mai tabbatar da cewa Jam’iyyar APC ce za ta yi nasara da rinjaye ta samu shugabancin Majalisar.”

Labarai Masu Nasaba

Kwana 2 Kafin Rantsuwa: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima

Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia

“A game da Batun Shiyya-Shiyya wacce uwar Jam’iyya ta ke kokarin shirin yi, mun san wani abu ne wanda ya saba wa ka’idar kundin tsarin mulkin Nijeriya domin sashe na 14 cikin 3, ya bayyana cewa ya kamata a raba mukamai bisa ga shiyyoyi ko Jihohi idan zai kai amma idan ba zai kai ba shi ne za a yi bisa ga shiyya-shiyya.

“Don haka wannan shi ne tsarin da muke da shi na Jagorancin shugabancin Kasa na shugaban kasa, shugaban Majalisar Dattijai da Majalisar wakilai Hakazalika da na mataimakan su wanda su ne guda shida domin kawo tsarin zaman lafiya da ingancin zamantakewa amma kamar an manta da wannan Dokar.”

“Ni dan Jam’iyya ne kuma na yarda da tsarin dokokin Jam’iyya kuma na tabbata idan Jam’iyya ta yi za mu yi kuma dama can yan Majalisa ne ke da hakkin yin zaɓe kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada kuma duk abin da ake yi ana tuntuba ne domin a ga yaya za a yi a kai ga nasara ta yadda ba za a samu hayaniya ba domin zaɓe ba ya gabata sai an Shiga cikin Majalisa.” In ji Shi.

Acewar Idris Wase, kamar yadda ya zo ya bayyana cewa yana neman shugabancin Majalisar, ai akwai wadanda su ma suka zo suna nema daga Jam’iyyarsu ta APC wanda suke da kyakkyawar alaka da tunani don haka ya kamata su hada kai su fitar da wanda suke ganin zai iya yin aikin daga cikin su shi yasa suke tattaunawa a kai.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Yancin Shari’a Na HK Ba Zai Bari Amurka Ta Rika Tsoma Baki Cikin Harkokin Yankin Ba

Next Post

Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Kasashen Sin Da Na Yankin Tsakiyar Asiya Ya Cimma Manyan Sakamako

Related

Kwana 2 Kafin Rantsuwa: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima
Siyasa

Kwana 2 Kafin Rantsuwa: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima

2 days ago
Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia
Siyasa

Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia

1 week ago
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti
Manyan Labarai

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti

1 week ago
Tinubu Da Kwankwaso Sun Gana A Faransa
Manyan Labarai

Tinubu Da Kwankwaso Sun Gana A Faransa

2 weeks ago
Zargin Dakatar Da Makarfi A PDP Tatsuniya Ce –Shugaba
Labarai

Zargin Dakatar Da Makarfi A PDP Tatsuniya Ce –Shugaba

2 weeks ago
Tsohon Dan Majalisar Tarayya, Ibrahim IMBA Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Siyasa

Tsohon Dan Majalisar Tarayya, Ibrahim IMBA Ya Sauya Sheka Zuwa APC

2 weeks ago
Next Post
Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Kasashen Sin Da Na Yankin Tsakiyar Asiya Ya Cimma Manyan Sakamako

Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Kasashen Sin Da Na Yankin Tsakiyar Asiya Ya Cimma Manyan Sakamako

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-dumi: Justis Hafsat Ta Rantsar Da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

Da Dumi-dumi: Justis Hafsat Ta Rantsar Da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

May 29, 2023
Da Dumi-dumi: An Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Nijeriya Na 16

Da Dumi-dumi: An Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Nijeriya Na 16

May 29, 2023
A Dan Lokacin Da Ya Rage Kafin Mika Mulki: Buhari Ya Sauya Sunayen Filayen Jiragen Sama 15

A Dan Lokacin Da Ya Rage Kafin Mika Mulki: Buhari Ya Sauya Sunayen Filayen Jiragen Sama 15

May 29, 2023
Ana Bin Jihar Kano Bashin Sama Da Naira Biliyan 240, Inji Abba Gida-gida 

Ana Bin Jihar Kano Bashin Sama Da Naira Biliyan 240, Inji Abba Gida-gida 

May 29, 2023
Bankwana Da Gwamnatin Buhari: Hukumar Tsaron Cikin Gida Ta Kara Wa Jami’ai 17,331 Matsayi

Bankwana Da Gwamnatin Buhari: Hukumar Tsaron Cikin Gida Ta Kara Wa Jami’ai 17,331 Matsayi

May 29, 2023
Gwamnati Ta Samar Da Tan 89,512 Na Irin Noma A Bana – Minista

Gwamnati Ta Samar Da Tan 89,512 Na Irin Noma A Bana – Minista

May 29, 2023
Kwana Guda Ya Sauka, El-Rufai Ya Haramta Kungiyar Kudancin Kaduna

Kwana Guda Ya Sauka, El-Rufai Ya Haramta Kungiyar Kudancin Kaduna

May 29, 2023
Buhari Ya Nada Sha’aban Mukamin Babban Sakataren Hukumar Kula Da Almajirai Ta Nijeriya

Buhari Ya Nada Sha’aban Mukamin Babban Sakataren Hukumar Kula Da Almajirai Ta Nijeriya

May 28, 2023
An Wallafa Littafin Dake Kunshe Da Mukalolin Shugaba Xi Kan Dogaro Da Kai A Fannin Kimiyya Da Fasaha

An Wallafa Littafin Dake Kunshe Da Mukalolin Shugaba Xi Kan Dogaro Da Kai A Fannin Kimiyya Da Fasaha

May 28, 2023
Ganduje Yayi Jawabin Bankwana Tare Da Shirin Mika Mulki A Yau Lahadi

Ganduje Yayi Jawabin Bankwana Tare Da Shirin Mika Mulki A Yau Lahadi

May 28, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.