Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce matsakaicin farashin litar dizal ya karu daga N828.82 a watan Janairun 2023 zuwa N1153.01 a watan Janairun 2024.
NBS ta bayyana hakan ne yayin da take bayyana farashin Dizal na watan Janairu 2024 da aka fitar a Abuja ranar Laraba.
- Wasu Mutum 2 Sun Mutu A Cikin Tankar Man Dizal A Kano
- Duro 350 Na Man Fetur Da Dizal Sun Kone Kurmus A Wata Gobara A Yola – Hukumar Kashe Gobara
Rahoton ya ce a watan Janairun 2024 farashin N1153.01 ya kai kashi 39.11 bisa 100 akan N828.82 da aka biya a watan Janairun 2023.
“A kowane wata, farashin ya karu da kashi 2.34 daga N1126.69 kowace lita da aka rubuta a watan Disamba 2023,” in ji ta.
Rahoton ya ce an samu matsakaicin farashin man dizal a watan Janairun 2024 a Kebbi kan Naira 1433.33 kan kowace lita, sai Kogi a kan N1300 sai Abuja a kan N1226.70.
Ya bayyana cewa an samu mafi karancin farashi a Borno kan N927.27 kan kowace lita, Kano sai N940.89 sai Taraba a kan N988.33.
“Kazalika, binciken da shiyyoyi suka yi ya nuna cewa yankin Arewa ta tsakiya ya fi kowacce lita farashin N1205.11, yayin da Arewa maso Gabas ta samu mafi karancin farashi a kan N1074.03.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp