Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wasu sojoji biyu na bogi da ake zargin sun yi barazanar kashe wani mutum da wuka a lokacin da suke fada da juna.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Legas ranar Laraba, ya ce wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda tun ranar Litinin.
- Babu Farfesan Bogi A Jami’ar Bayero Ta Kano – Shugaban Jami’a
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Kwamiti Don Binciko Digirin Bogi
Hundeyin ya ce, rundunar ‘yan sanda ta Isolo a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 10:30 na rana, ta samu labarin cewa an yi rikici a titin Aina, unguwar Isolo a Legas.
Ya ce nan take aka tura tawagar ‘yan sintiri zuwa yankin domin kwantar da hankali da zaman lafiya a yankin.
Ganau a wajen ya ce a lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin, sun gano cewa an ga wani mai suna Ben Okafor, wanda ya yi ikirarin cewa shi jami’i ne a rundunar sojojin Nijeriya dauke da wukar a jikinsa tare da wani mutum mai suna Darlinton Ihenacho.
Hundeyin ya ce an ga mutanen biyu suna fada da wani Oludotun, wanda daga baya ya kai karar ga ‘yan sanda cewa wani soja yana binsa da wuka yana masa barazanar kashe shi.
“Bayan an kama wadanda ake zargin tare da bincikar su, an gano wani katin shaida na Sojojin Nijeriya na bogi, mai dauke da Cpl. Geoffrey Emmanuel, mai lamba 140861 da wuka da barkonon tsohuwa da aka samu a hannunsu.
“Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.