Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce yankin kudancin tekun Pasifik, ba zai zamo dandalin hamayyar manyan kasashe masu karfin fada a ji ba.
Wang ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin taron manema labarai da ya gudanar tare da takwaran aikinsa na Papua New Guinea Justin Tkatchenko lokacin da ya ziyarci kasar. Ya ce ba wata kasa dake da ikon mayar da wata kasar dake yankin fagen da za ta iya yin duk abun da take so.
A wani ci gaban kuma, Wang Yi ya ce gaggauta amincewa da bukatar Falasdinu ta zama mamba a MDD, mataki ne da zai gyara rashin adalci na tsawon lokaci da aka tafka a tarihi. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp