Kamfanin hakar mai na teku na kasar Sin (CNOOC) ya sanar a yau Lahadi cewa, yankin rijiyoyin mai na teku na Bohai mafi girma na kasar Sin, ya samar da fiye da tan miliyan 40 na mai a shekarar 2025, inda hakan ya kafa sabon tarihi.
A cewar CNOOC, a matsayin yankin na wanda yake kan gaba a bangaren rijiyoyin mai na teku ta fuskar yawan hakowa da mizani, adadin da aka samu na yawan mai da iskar gas da ya hako zai samar da cikakken goyon baya ga samun wadatar makamashi a cikin kasa da ingantaccen ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Yankin rijiyoyin mai na teku na Bohai, wanda a halin yanzu yake gudanar da aiki a fiye da rijiyoyin mai 60 da ke samar da mai da iskar gas, ya hako yawan danyen mai da ya haura tan miliyan 600. A cikin shekaru biyar da suka gabata, yawan man da yake hakowa da kuma iskar gas da yake samu ya ci gaba da karuwa da kashi 5 cikin dari a duk shekara, kamar yadda CNOOC ya bayyana.
Kamfanin ya ce, yankin mai na teku na Bohai yana kuma ci gaba da sauye-sauye a bangaren fasahar zamani da samar da ci gaba mara gurbata muhalli, kuma an samu sabbin nasarori wajen zakulo muhimman kayayyakin aiki, ciki har da fara aiki da wani tsarin injunan samar da mai ta karkashin teku mara zurfi da kasar Sin ta kera a cikin gida karon farko. A halin yanzu kuma, an sada hanyoyin samar da lantarki na kan-tudu da sama da kashi 80 cikin dari na rijiyoyin mai na teku na Bohai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














