Daruruwan mutane ne suka halarci taron bikin bauta na Fuxi, wanda yake zaman kakan al’adun gargajiyar kasar Sin, a birnin New Taipei na yankin Taiwan na kasar a yau Asabar.
An gudanar da taron bautar ne a daidai lokacin da aka yi irinsa a birnin Tianshui dake arewa maso yammacin lardin Gansu, inda ake kyautata zaton a nan ne aka haifi Fuxi.
Wannan dai ita ce shekara ta 12 a jere da al’ummomin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ke gudanar da bukukuwan bauta a lokaci guda ga fitaccen jarumin, tun bayan da aka fara gudanar da ire-iren wannan bikin a shekarar 2014. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp