Rundunar ‘yansandan Jihar Borno ta bayyana cewa, sun samu nasarar kama wani dattijo mai suna Saleh Bukar mai shekara 80 a duniya a bisa laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 11 fyade.
Kwamishinan ‘yansandan, Abdu Umar, ya bayyana haka ne ranar Laraba a lokacin da yake gabatar da Dattijon tare da wasu mutum 6 da ake zargi da aikata fyade a Maiduguri.
Kwamishinan ya ce, ‘yaruwar yarinyar da aka yi wa fyaden ne mai suna Fatima Ali, ta fahinci yadda wani abu ke fatowa daga farjin yarinyar, daga nan ne ta tuhumi yarinyar, inda ta bayyana wa Fatima dukkan abin da ya faru har da yadda Bukar ya yi ta mata fyade a lokutta daban daban.
Kwamishinan ‘yansandan ya ce, da zaran jami’ansa sun kammala bincike za su gabatar da dattijon gaban kotu don a yanke musu hukuncin da ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp