Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadik, ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan wani harbin da wani jami’in ‘Cibilian Joint Task Force’ ya yi wanda ya yi sanadin mutuwar dalibin jami’ar tarayya mai matakin karatu na 400 da ke Dutsinma a jihar domin cafke wanda ya aikata laifin.
Sadik ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Katsina.
- Japan Ta Kirkiro Da Sabuwar Kimiyyar Samar Da Ingantacciyar Madarar Shanu
- Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa
A cewar sanarwar, “Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta fara gudanar da bincike kan wani harbin da wani jami’in rundunar hadin gwiwa na Cibilian Task Force ya yi. Lamarin ya yi sanadiyar raunata wani direban okada da kuma mutuwar wani dalibi mai mataki 400 na jami’ar tarayya ta Dutsinma.
“Rahotanni na farko sun nuna cewa, a ranar 23 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 11:26 na safe, wani direban babur na haya da ke jigilar fasinja, Sa’idu Abdulkadir, ya hadu da tawagar CJTF a cikin motar Hilud. Daya daga cikin ‘yan JTF din ya yi harbin kan wadanda lamarin ya rutsa da su, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mai babur din.
“Ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yansanda suka kai dauki inda suka garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Dutsinma. Daga baya aka mika Sa’idu asibitin kashi na Katsina, inda aka tabbatar da cewa ya rasu da isarsa.”
Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su.
Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji shi.
Tun da farko dai, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne mahukuntan jami’ar suka rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan abokin aikinsu.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu a Katsina a safiyar ranar Litinin cewa, “wasu jami’an CJTF sun bindige dalibai biyu ne bisa kuskure, suna tunanin ‘yan fashi ne.
“Daya daga cikin daliban ya mutu nan take yayin da daya kuma aka harbe shi a kafa, kuma tuni aka kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
“Bayan wannan ci gaba, dalibai sun shiga zanga-zanga tun jiya lokacin da lamarin ya faru, inda suka fito kan tituna a Dutsinma, suna kona motoci tare da lalata dukiyoyi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp