Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi ta ƙaryata rahotannin da ke cewa wasu fusatattun matasa sun ƙone gidan Shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓar Ribina ta Yamma, a ƙaramar hukumar Toro.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne bayan cece-kuce kan sarautar gargajiya da ake son mayarwa daga garin Koginsallah zuwa wani gari, inda ake zargin cewa an ƙone gidan shugaban PDP yayin zanga-zangar.
Sai dai kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce labarin ƙarya ne da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.
Ya bayyana cewa suna samu rahoton, Kwamishinan ’Yansanda, CP Sani Omolori Aliyu, ya umarci DPO da kwamandan yankin Toro suka tura jami’ai domin hana tashin hankali.
An kuma gudanar da taron zaman lafiya tare da Sarkin Toro da sauran shugabannin gargajiya, inda suka tabbatar cewa babu sabon hakimin da aka naɗa, kuma labarin ƙarya ne.
Wakil, ya gargaɗi masu yaɗa labaran ƙarya da su daina, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci bisa dokar laifuka ta amfani da kafafen sadarwa.
Ya tabbatar da cewa ba a ƙone gidan shugaban jam’iyyar PDP ba, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.
Ya shawarci mazauna yankin da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, yayin da hukumomi ke ci gaba da sanya ido kan lamarin.














