Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta cafke wasu ‘yan sanda hudu da suka hada da babban jami’i daya da kuma sifetoci uku bisa zarginsu da hannu dumu-dumu a cikin magudin zabe a jihar.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda ‘yan sandan ke aiki a cikin motar Hilux mai lamba ‘RRT 050’, suna sace kayan zabe a wani wuri da ba a bayyana ba a jihar.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, Grace Iringe-Koko, a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Fatakwal a ranar Litinin, ta ce an kama motar domin gudanar da cikakken bincike.
“Rundunar ‘yan sandan ta bukaci mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu su jira a sanar da sakamakon zaben a hukumance,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp